Daga Awwal Umar Kontagora Sabuwar ƙungiyar 'yan banga 'Vigilante Group Of Nigeria' ta nemi al'umma da su hada da...
Daga Awwal Umar Kontagora
Sabuwar ƙungiyar 'yan banga 'Vigilante Group Of Nigeria' ta nemi al'umma da su hada da gwamnati da sauran sassan tsaro hadin kai wajen aiwatar da ayyukansu dan samun ingaantacce tsaro a kasa.
Kwamandan VGN a jihar Neja, Kabiru Usman Kudu tsohon jami'in sojan ruwa ( AWO) mai ritaya ne yayi kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai a minna.
Kwamandan yace gwamnati ba za ta samu nasara ba a yaki da yan ta'adda, garkuwa da jama'a, fadan makiyaya da manoma, fadan daba, da fasa bututun mai dole sai an samu hadin kan al'umma.
Ya ce mu babban aikin mu shi ne tabbatar da zaman lafiyar al'umma, kare dukiyoyin kasa da na al'umma, hakan zai ba mu damar samun zaman lafiya a kasa.
Mun samu kan mu a koma baya ta fuskar tsaro da yawaitar rikice rikicen matasa sakamakon rashin samun cikakken goyon bayan al'umma wanda dole mu hada kai da gwamnati wajen ceto kasar nan daga halin da take ciki ta fuskar hada hannu da masu kishin kasa dan samar da zaman lafiya da takaita aikata laifuka, da haka ne kawai za a samu zaman lafiya kamar yadda ake a baya.
Muna da bangarorin tsaro da dama, kuma kowa na da rawar da yake takawa dan haka akwai bukatar duk wanda ya ga wani abinda ba daidai ba, ya gaggauta sanar da jami'a tsaro dan daukar matakin gaggawa.
Dangane da kishiyar kungiyar sintiri a jihar Neja kuwa, yace kafin zuwan mu akwai kungiyoyin sintiri da dama, mafi fice a cikinsu itace kungiyar Nigeria Vigilante Crops wadda Malam Nasiru Mohammed Manta ke jagoranta, muna mika hannun mu biyu da su zo mu hada kai dan yin aiki yadda ya dace, ba tare da nuna bambanci ko hantarar juna ba.
Jihar Neja na da fadi sosai da yawan al'umma, kuma dukkan mu yan jiha dokar kasa ta ba mu damar yin aiki tare ya kamata mu hada kai da manyan rundunonin tsaro dan tabbatar da zaman lafiya da dakile duk wani abinda zai zamo barazana ga zaman lafiyar al'umma.
Rundunar VGN tana da jami'ai da ke aiki ba dare ba rana duk da cewar ba mu jima da shigowa a kasa ba, amma a shirye muke dan tsaftace kasar nan da yin aiki tukuru kamar yadda aka horar da mu.
Aikin ni ba sabo ba ne a cikinta, na yi aiki da rundunar sojan ruwan Nijeriya kuma har na kai ga matsayin yin ritaya bayan kai ga matsayin AWO a tsarin aikin soja.
No comments