Daga Awwal Umar Kontagora Ƙungiyar matasa ta 'Fulbe Youth Association of Nigera' da haɗin guiwar Fulbe Youth Sai Bago Ag...
Daga Awwal Umar Kontagora
Ƙungiyar matasa ta 'Fulbe Youth Association of Nigera' da haɗin guiwar Fulbe Youth Sai Bago Again Organisation sun taya Alhaji Muhammad Babangida, Daraktan gudanarwa na El-Amin International Schools kuma Shugaban ƙungiyoyin wasan dawako (Polo) na Minna da Kaduna, murna bisa nadin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi masa a matsayin Shugaban Bankin Noma (Bank of Agriculture) da aka sake fasaltata dan inganta harkokin noma a kasar nan.
A cikin wata sanarwa daya samu sanya hannun shugaban kungiyar Amb. Dr. Mujahid Adam da sakataren kungiyar Kwamred Sulaiman Ruga, aka rabawa manema labarai a Minna, takardar ta bayyana cewa nadin Mohammed Babangida ɗa tsohon shugaban ƙasa a mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida abin alfahari da cigaba mai anfani ga harkar noma a kasar nan duba da irin rawar da yake takawa a bangarori da dama.
Fulbe Youth Association da hadin guiwar Fulbe Youth Sai Bago Again Organisation sun yi godiya ga shugaba kasa Bola Ahmed Tinubu bisa ga zaben da ya yi na Alhaji Muhammadu Babangida, wanda matashi ne mai kwazo wanda yasan aiki kuma sun bayyana goyon bayan su ga shugaban rawar da yake takawa na daidaita lamurran noma da kiwo a kasar nan.
Kungiyoyin sun bada tabbacin cewa nadin da aka yi wa Alhaji Muhammad Babangida a matsayin shugaban Bankin Noma zai taka muhimmiyar rawa wajen farfaɗo da harkar noma da kiwo a jihar Neja da ƙasar nan baki ɗaya ta yadda tattalin arzikin kasar zai bunkasa.
Ya ƙara da cewa, dukkan mambobin ƙungiyar sun nuna alfaharin su da wannan matsayi da aka ba Alhaji Muhammad Babangida, tare da yi masa fatan nasara da cikakken aiki mai albarka a sabuwar matsayin.
No comments