Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An gano ƴan matan da ƴan bindiga suka sace ɗauke da juna biyu jihar Neja

Daga Awwal Umar Kontagora Rahotanni sun tabbatar da ceto wasu yan mata da yan bindiga suka yi garkuwa da su dauke da ciki. Yan m...

Daga Awwal Umar Kontagora

Rahotanni sun tabbatar da ceto wasu yan mata da yan bindiga suka yi garkuwa da su dauke da ciki. Yan mata da aka yi garkuwan da su sun fito daga ƙananan hukumomin Rafi da Shiroro na jihar Neja tun watan Fabrairu 2024. Suka samu damar kubutowa daga hannun yan bindigar, da dama daga cikinsu rahotanni sun tabbatar da cewar suna dauke da juna biyu, yayin da wasun suka dawo da jarirai.

Rahotanni sun tabbatar da cewar juna biyun da jariran da matan ke ɗauke da su na yan bindigar ne da suka tsare su fiye da shekara guda, kafin jami’an yan sanda su ceto su.

Rahotannin sun shaida cewar an gano cewa huɗu daga cikin su na dauke da ciki, cikin yan mata ashirin da biyar da aka yi garkuwa da su kauyen Allawa, a kan hanyar Pandogari-Allawa, yayin da suke dawowa daga kasuwa cikin watan Fabrairu 2024.

Wasu rahotanni dai sun ce yan bindigar sun ɗauko matan da yawansu ya kai ashirin da biyar daga Palu-Waya a karamar hukumar Shiroro a cikin motocin haya, inda suke ƙoƙarin mayar da su wani matsugunni na daban.

Da suka iso yankin Kagara a karamar hukumar Rafi, wata daga cikin matan ta nemi izinin yin lalura. Lokacin da aka tsaya, sai ta ankarar da jama’a tare da neman taimako wanda hakan ya jawo hankalin jama’a, kuma hakan ne yasa aka ceto su daga hannun yan bindigar tare da cafke direban motar da yanzu haka ya ke hannun jami'an tsaro.

Wata majiya daga rundunar yan sanda ta jihar Neja da ke Minna ta tabbatar da cewa yanzu haka matan na karkashin kulawar rundunar, kuma an gano makamai a cikin jakar ɗaya daga cikin matan.

Majiyar ta tabbatar cewa ɗaya daga cikin waɗanda aka ceto tana cikin yan matan Chibok da aka dade ana nema, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
Koma dai da me, yan bindigar na cigaba da baje kolinsu a jihar Neja, ko a farkon satin nan sai da suka farmaki mutanem Rijau shalkwatan karamar hukumar Rijau, inda bayan rahoton harbe wata mata a safiyar littinin din makon nan, yayi da ake tuhumar sace wasu mutanen gari bayan tsarewa da mutane suka yi dan neman mafaka.

Yan bindigar bayan sun samu nasarar tattara shanayen wasu da suka, labarar makon nan an samu rahoton bullarsu a garin Mariga inda bayan dauki ba dadi da jami'an tsaro, jami'an tsaron sun yi nasarar karbe wasu dabbobin da yan bindigar suka sato, inda yan bindigar su kayi sansani a kauyen Adunu.

Zuwa hada rahoton dai a safiyar alhamis din nan ba a san halin da mutanen karkara da suka shafi Rijau, Mariga da Mashegu ke ciki ba sakamakon watsuwan da yan bindigar su kayi a cikin dazukan ba.

No comments