Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tinubu ya fara tunanin jam'iyyar da zai yi takara dan mai APC ya tafi da kayan shi - Wana

Daga Awwal Umar Kontagora An bayyana cewar rashin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari rashi ne da ya kamata gwamnatin tarayya...


Daga Awwal Umar Kontagora

An bayyana cewar rashin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari rashi ne da ya kamata gwamnatin tarayya ta nuna kaduwarta gaya. Amma abinda gwamnatin Tinubu ta nuna rashin Muhammadu Buhari tamkar rashi ne da ya shafi yan Arewa kadai.

Wani jigon a jam'iyyar APC kuma daya daga cikin dattijan da suka goyawa takarar shugaba Tinubu a 2023 da ya gabata, Alhaji Awaisi Giwa Wana ( Wakilin Gwari-Nupe) ya bayyana hakan lokacin da yake nuna takaicinsa kan rashin ko in kula da ya zargi gwamnatin Tinubu akan rasuwar tsohon shugaban kasar.

Wana, ya cigaba da cewar Muhammadu Buhari ya shugabanci kasar nan a mulkin soja, kuma Allah ya sake jarabtarsa da dawo shugabanci a matsayin farar hula, yau bambancin shugaba Tinubu da marigayi Muhammadu Buhari bai wuce kariya, sauran kasashe kan tsayar da duk wasu al'amurran yau da kullun idan aka yi rashi irin wannan.

Jam'iyyar APC gadon marigayi Buhari kuma ya tafi da kayan shi, saboda haka Tinubu ya fara tunanin jam'iyyar da zai takara a gaba, domin wanda ya assasa APC ya tafi da kayan shi. Abinda muka fahimta yanzu mun yi kuskure babba a zaben da ya gabata, amma zabe mai zuwa zamu tabbatar mun yi abinda ya dace.

Peter Obi ya san inda kuri'arsa za ta fito idan ya tsaya 2027, mu yan arewa da muka baiwa gwamnatin Tinubu kuri'a fiye da kowani shiyya mu ne aka watsar kuma abinda ya shafi arewar bai da muhimmanci a wannan gwamnatin. Daman daraja da dattijantaka yasa muka marawa shugaba Tinubu, amma yanzu kan mage ya waye kuma za mu tabbatar mun da yan uwan mu muhimmin matakin da ya kamata mu dauka, kuma kai wajen zaben kishin kasa ba yankin shi da kabilar shi ba.

Saboda haka, ina kira ga yan siyasar arewa da mu ajiye bambancin jam'iyya mu tabbatar mun hada kai wajen marawa mutanen da ke kyautata gaskiyarsu da kaunar wanzuwan a matsayin kullalliya.

Lokaci yayi da za mu tabbatar da cewar kuri'un mu sun tafi a inda yafi cancanta ga dan takarar da ke kishin kasa wanda bai siyasar kabilanci kuma wanda ya shirya wajen ceto rayuwar talaka, da bautawa kasa da gaskiya. Idan yan arewa suka cigaba da zaben shugabannin da ba su da kudurin da ya wuce kan su da yan uwansu sai mun wayi gari a arewa ba sauran iskar da za mu shaka.

Tinubu, mu yan arewa ke son shi amma maganar gaskiya bai son mu, matsalar tsaro, tsadar rayuwa da hauhawar kudin shigar da zara a aljihun talakan da bai san abinda ake yi da kudaden da ake tatsa a cikin aljuhun shi kawai ya isa ya nuna ma cewar gwamnatin Tinubu ba ta san inda ta sanya gaba ba.
Buhari, ya shugabanci kasar karo biyu, kuma kowa shaida ne mulkinsa ba mulkin bangaranci ba ne hakan yasa lokacin da aka yi hadaka bayan kafa mulki ya tabbatar a gwamnatinsa kowa ya samu wakilci sabanin abinda muke gani yau a wannan mukiin.

Yanzu dai ta nuna karara ba APC ke mulki ba, ana yi mana mulkin ungulu ne da kan zabo, mun yarda hadakar APC ta watse, domin wanda aka yi hadakar domin shi ya kammala kuma yafi da kimar APC din da yan APC na gaskiya.

No comments