Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Matsalar Ruwa: Al'umma sun nemi gwamnatin Neja ta dubi lamarin ma'aikatar ruwa ta jiha

Daga Awwal Umar Kontagora Tun kafin saukar ruwan sama jama'ar cikin garin Minna ke kokawa kan matsalar rashin samun tsaftaccen ruwa sha ...


Daga Awwal Umar Kontagora

Tun kafin saukar ruwan sama jama'ar cikin garin Minna ke kokawa kan matsalar rashin samun tsaftaccen ruwa sha daga hukumar samar da ruwa ta jiha, wanda a lokacin rahotanni sun tabbatar da cewar gwamnatin jiha ta sha alwashin magance wannan matsalar wanda a lokacin gwamnatin ta bayyana kudurinta na samar da wasu hanyoyin da hukumar kula da harkokin samar da ruwa za ta bi dan saukakawa al'ummar cikin garin Minna gwamnatin jiha za ta samu sauki musamman ganin a lokacin masu sayar da ruwan kura ( Baro) na cin karen su ba babbaka ta tsawwala kudin kurar ruwa akan dubu biyu zuwa duba daya da dari biyar.

Wani mazaunin unguwar Maitumbi da ya nemi a sakaya sunan sa yace duk ruwan sama ya sauka ba abinda ya canja dangane da batun ruwan sha a Minna, domin yanzu da yake lokacin damana ne kuma ruwan ba kowani lokaci ake yin shi muna sayen ruwan kura akan dubu daya da dari biyu zuwa dubu daya da dari biyar, wanda hukumar ruwa ta jiha ta mayar da hankali da mun samu sauki akan matsalar ruwan sha a cikin garin Minna.

Alhaji Muhammadu Lawal Ibrahim ( Hamdala) wani mazaunin Minna, yace maganar gaskiya muna ji a jikin mu.

Ya cigaba cewar mu yanzu da ke zaune a yankin Custom Barrak muna sayen ruwa akan dubu daya da dari biyar zuwa dubu biyu. Ka ga talaka mai karamin karfi da ke fafuka abubuwan na mana yawa.

Lokacin baya kafin saukar damana mun ji labarin cewar gwamnati ta fara yunkurin daukar mataki amma tunda ruwan sama ya sauka mun ji shiru. Ruwan saman ba koda yaushe ake yinsa ba, kuma su kan su masu sayar da ruwan da daman su sun koma saboda fuskantar noma.

Mun samu labarin ayyukan hanyoyi da gwamnati ta sanya a gaba shi ya janyo wannan matsalar saboda taushewar wasu hanyoyin da hukumar ruwa ke anfani da su wajen baiwa jama'a ruwan sha.

Ba mu ce a daina aikin ba, dan ayyuka ne na cigaban kasa da muka dade muna tsimayen su, amma ya kamata a ce an samar da wasu dubaru dan gudun bacin rana irin wanda muke ciki yanzu.

Ina shawarta maigirma gwamna, a matsayinsa na jarumi kuma mai kwazo da ya lalubo wasu hanyoyin da za a saukakawa rayuwar al'ummomin cikin garin Minna akan wannan matsalar ta ruwan sha.

Har yanzu hukumar ruwa tana turo mana bill na ruwa duk da cewar ba ma samun ruwan, wanda hakan na iya janyo koda an dawo da bada ruwan jama'a su ki bada hadin kai wajen biyan kudi, wanda kuma za mu so hakan ta faru ba. 


No comments