Daga Awwal Umar Kontagora Sakamakon gudunmawa da rawar da Fulani makiyaya suka bayar a manyan zabukan kasa da suka gabata na 202...
Daga Awwal Umar Kontagora
Sakamakon gudunmawa da rawar da Fulani makiyaya suka bayar a manyan zabukan kasa da suka gabata na 2023, gwamnan jihar Neja, Dakta Umaru Mohammed Bago ya sha alwashin ganin ya janyo Fulani makiyaya kusa da gwamnati dan samun damar jin matsalolin su tare alkawali kafa ma'aikata musamman wanda za a ba su damar jagorantar ta.
Gwamnan, ya cika wannan alƙawarin wanda yanzu wannan ma'aikatar da aka yi wa laƙabi da 'Ministry of Nomadic an Postral Affairs', wanda tun bayan kafa ma'aikatar tazo da tsare tsare masu muhimmanci wanda za a yi ma ta sambarka musamman a yunkurinta na dawo da martabar ilimin yayan makiyaya.
A jihar Neja, kusan a sassa uku na jihar akwai makarantun Nomadic sama da dari da kafuwarsu, wasun su sun yi dogon suma ba sa motsi, yayin da wasu makarantun da dama suna raye amma matsalolin da ya da baibaiye su yasa duk da cewar suna motsi amma ba su da wani tasirin da za a yaba.
Kan haka, kwamishina a ma'aikatar, Hon. Umar Sanda Rebe yai ziyarar gani da ido tare da tattara bayanai da yace zai mikawa hukumar SUBEB dan bada agajin gaggawa ga shirin gwamnatin jiha.
Duk da damanmakin da gwamnatin jiha ke bayarwa idan ba a samu ginshiki na kwarai ba sai dai shirye shiryen su kare a takardu ba tare da samun nasarar da ake bukata ba. Misali matsalar lalacewar makarantun sakamakon dadewarsu, da matsalar rashin malamai masu karantarwa zai iya sanya duk wani yunkuri na sanya yara makaranta zai citura, domin koda an sanya yaran ba wani abin azo a gani za su samu ba dangane da neman ilimin ba.
GAMU Nomadic primary school da ke yankin Maikunkele a karamar hukumar Bosso ta isa misali kuma kashi tamanin da biyar zuwa tis'in haka suke, azuzuwan sun lalace, rufin sama ya kware kuma kusan wasu sassan gine-ginen barazana ne ga rayuwar daliban.
Kusan shekaru biyu tun bayan kafuwar gwamnatin da sabuwar ma'aikatar ake yekuwar farfado da ilimin yayan makiyaya. Tilas, idan da gaske ana neman dawo da martabar ilimin nan, bayan gwamnati ta bada gudunmawa, akwai bukatar masu ruwa da tsaki, sarakunan Fulani da kungiyoyi masu zaman kansu su taka na su rawar.
Yau, da zuwan gwamnatin nan, Fulani makiyaya sun samu sarautun gargajiya da dama, an gudanar da bukukuwan nade-nade karkashin kulawar wannan ma'aikatar kuma bisa jagoranci maigirma kwamishina.
Amma har yanzu ba wata makarantar Nomadic daya da kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders, ko Kautal Hore, ko kuma Gan-Allah Fulani Social Cultural Association suka bugi kirji suka gina ko gyara ba, balle a ce an yi bukin nadin Dikko ko Ardo tare da bude makarantar ba.
Saboda mutunci da girmamawa ga harshen fulatanci, gwamnatin jiha ta ware rana na musamman dan tunawa da harshen fulatanci, ya kamata tunda an kaddamar masu ruwa da tsaki su yi tsayin daka wajen ganin an ceto ilimin yayan makiyaya musamman mazauna karkara ta hanyar farfado da martabar makarantun gurin samar masu kayan aiki da ajujuwan da yara za su rika daukar darasi ba tare da fargaba ko fashi ba.
Hadakar kungiyoyin Fulani guri daya abu ne mai kyau, da zai samar da hadin kai, kishi da kuma ganin wannan sabuwar ma'aikatar da aka ba su amana ta dore.
No comments