Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, Shugaban rukunin jami’o’in MAAUN, zai karɓi lambar yabo mai daraja ta “Trailblazer in Tertiary Ed...
Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, Shugaban rukunin jami’o’in MAAUN, zai karɓi lambar yabo mai daraja ta “Trailblazer in Tertiary Education Award” daga Jaridar Blueprint dake Abuja a wani babban taron da za a gudanar gobe Litinin a birnin na Abuja.
Za a ba da kyautar ne a wani babban biki da zai haɗa manyan jami'an gwamnati daga sassa daban-daban na ƙasar nan, ciki har da Gwamnoni, Ministoci, masu ruwa da tsaki, da sauran fitattun shugabanni na ƙasa. Wannan bikin na shekara-shekara na nufin girmama mutanen da suka taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban ƙasa.
An zaɓi Farfesa Gwarzo domin bayar da wannan lambar yabo saboda irin gagarumin gudummawar da yake bayarwa wajen sauya fasalin tsarin ilimin jami’a a Nijeriya da ma wasu ƙasashen Afirka.
Rahotanni sun nuna cewa a ƙarƙashin shugabancinsa, rukunin jami’o’in MAAUN ya ci gaba da bunƙasa tare da samar da ingantaccen ilimi ga ɗalibai.
A cewar hukumar Jaridar Blueprint, wannan lambar yabo na nufin karrama Farfesa Gwarzo saboda jajircewarsa wajen inganta harkar ilimi, samar da ci gaba a fannin kimiyya da horar da matasa domin ciyar da ƙasa gaba.
Za a gudanar da bikin bada kyaututtuka a fannoni daban-daban, ciki har da ɓangaren nagarta a shugabanci, kyakkyawan aiki a gwamnati, da ci gaba a fannin ilimi, inda Farfesa Gwarzo zai samu wannan girmamawa tare da wasu fitattun 'yan Nijeriya daga ɓangarori daban-daban.
No comments