Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Aliyu Shehu Ya Zama Zakaran Gasar Badminton Na Kofin Umar Bago A Neja

Daga Awwal Umar Kontagora Gwamnatin Neja ta tallafawa kungiyar kwallon Badminton ta kasa da naira miliyan goma dan karfafa kungi...

Daga Awwal Umar Kontagora

Gwamnatin Neja ta tallafawa kungiyar kwallon Badminton ta kasa da naira miliyan goma dan karfafa kungiyar wajen cigaba da yin gogayya da sauran kasashen duniya. Gwamnan jihar Neja, Manomi Umar Mohammed Bago ne ya bayyana hakan a lokacin bukin kammala gasar kwallon Badminton da aka gwabza tsakanin kananan hukumomin jihar Neja, gasar wanda ya samu halartar kananan hukumomi goma sha takwas cikin ashirin da biyar da ake da su a jihar.

A jawabinsa, shugaban kungiyar ta kasa Badminton Federation of Nigeria, Mr. Francis Orbih, ya yabawa kungiyar ta jihar Neja, Badminton Assocition na jihar Neja da gwamnatin jiha wajen shirya wannan gasar, inda ya bayyana cewar jihar na daga cikin jahohin da tarihi ya nuna kan gaba wajen Kwallon Badminton, wanda yace dan wasa na biyu da kasar nan ke alfahari da su daga jihar Neja ya fito kuma ya taka rawar gani wajen halartar wasanni da dama a nahiyar Afrika da sauran sassan duniya da kasar ta halarta wanda hakan ya ba shi damar zama gwarzo na biyu a kasar nan da ake alfahari da su wato Aliyu Shehu.

Ba a bin mamaki ba ne da ya zamo zakara wajen zama na daya a wannan gasar, kasancewarsa tsohon hannu da yasan makaman aiki, shi kan shi Baba Aliyu Sa'idu da ya zamo na biyu a fafatawar ya nuna nan gaba zai iya jigon da kasar nan za ta yi alfahari da shi a wasan kwallon Badminton.


Mr. Francis, ya yabawa kungiyar reshen jihar Neja, kan samar da tsayayyen dakin wasan da ko a wasan kasa ana iya gwabzawa a nan. Dan haka a shirye muke idan gwamnatin Neja ta shirya za mu kawo wasan kasa a jihar nan.

Malam Muhammad Nma Kolo ( Jawon Minna kuma Amanan Lapai) shugaban kungiyar a Neja, yace manufar kungiyar na shirya gasar a bangaren kananan hukumomi, shi ne yunkurin kungiyar na zakulo barada a bangaren kwallon Badminton a yankunan karkara, wannan dakin wasan Badminton shi ne irinsa na farko bayan dakin wasa ta kasa, kuma dukkanin abinda yan wasa ke bukata an tanade su, dan karfafa guiwar kwallon Badminton a jihar Neja.

A yau mun kammala gasar a bangaren mata da maza kuma mun samu nasarar da muke bukata, domin mun samu karin zakarun da za mu mayar da hankali a kan su.

Jawon Minna, ya nemi masu ruwa da tsaki da su zuba jarinsu a wannan bangaren domin yana daga cikin bangaren wasanni da duniya ke tutiya da shi, hakan zai bada damar karfafa guiwar matasa wajen rungumar kwallon Badminton ka'in da na'in ta yadda za a kawo karshen zaman kashe wando ga matasa, da kuma samar da kiwon lafiya ga manya masu shekaru.
Da yake bayani, gwwarzon wasan, Aliyu Shehu, yace bai yi mamakin samun nasarar wasan ba, domin ya fafata a wasanni da dama kuma ya samu nasara, dan haka ba wani abu ba ne face jajircewa da mayar da hankalinsa akai, ina jawo hankalin yan uwana da muka gwabza a bangarori daban daban, da su dauka nasara ta nasarar mu ce baki daya, su taho mu hada kai dan ciyar da kwallon Badminton gaba.

An dai gwabza ne tsakanin Aliyu Shehu da Baba Aliyu Sa'idu inda a wasan farko da na biyu an tashi da cin kwallo 21 da 17 a wasanni guda biyu.

Mata da maza a bangarorin wasan da aka buga sun samu nasarar tashi da lambar Silba da Tagulla.

An gwabza gasar ne cikin kwanaki hudu, a babban dakin wasan na kasa da ke hanyar David Mark da ke cikin garin minna.
Tsohon mataimakin gwamnan Neja, Hon. Muhammad Ahmed Ketso, da shugaban ma'aikatan jihar, da kwamishinan kudi Hon. Muhammad Lawal Maikano ya kasance cikin yan kwallon da suka buga wasar da sauran manyan jami'an gwamnatin jiha sun nuna farin cikin su a wannan gasar a karon farko da kungiyar ta shirya tsakanin kananan hukumomin jihar.

No comments