Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Halin Da Ake Ciki Na Matsin Rayuwa Alamar Nasara Tana Tafe - Barr. Alfa

Daga Awwal Umar Kontagora An bayyana cewar halin da ake ciki yanzu na matsin rayuwa alamar nasara tana tafe duba da irin barnar ...


Daga Awwal Umar Kontagora

An bayyana cewar halin da ake ciki yanzu na matsin rayuwa alamar nasara tana tafe duba da irin barnar da gwamnatin da ta shude tayi. Barista Alfa Mohammed, jami'in yada labarai na jam'iyyar SDP ya bayyana hakan a wani tsokacin da ya yiwa manema labarai a Minna.

Ya ce matsalolin da aka gadarwa gwamnatin Bola Ahmad Tinubu, idan ba dan yazo da kyakkyawar niyya da samar da hanyoyin gyara ga yadda ake mulkin kasar nan, da yanzu kasar nan ba mu san matsayin mu ba. Domin wadanda suka samu damar mike kafa a gwamnatin da ta shude, sun aikata abubuwan da suka ga dama ba tare da fargabar wani abu zai iya biyo baya ba.

Lauyan, ya cigaba da cewar kiranyen da jama'a ke yi na a bude iyakokin kasar nan, bai gamsu da su ba, inda ya kwatanta kasar China ba samu damar tsayawa a matsayin da take ba yau sai da ta tabbatar ta kulle dukkanin iyakokinta, abinda kasar ke samarwa da shi yan kasar suka dogara ga shi yau sun mamaye duniya.

" Gwamnatin Tinubu na da kudurin dawo da martabar noma, wanda idan aka bada damar cigaba da shigo da abinci lallai zai zama kudurin gwamnatin ba zai cika ba kuma za mu cigaba da dauwama a inda muke, sannan manoman mu ba zasu samu kwarin guiwar cin ma manufar da ake bukata ba, domin zai zama shirin bai da alfanu.

Abin bakin ciki da takaici, irin kudaden da hukumomin da kula da alhakin karbo kudaden da aka sace na gwamnati ke karbowa a hannun barayin, ya isa ya tabbatar maka cewar dukkanin basussukan da gwamnatin da ta gabata tayi, ba a yi anfani da su yadda ya dace ba, kuma kamar dama ce kawai ta baiwa barayi suka yi ta wawuran dukiyar kasa, wanda yanzu gwamnatin da ta gaje ta take kokarin tsalkake kasar daga wannan mugun halin da marasa kishin kasa suka jefa ta.

Muna maganar man fetur wanda kusan da shi muka dogara kuma dukkanin basussukan da aka karbo da man da ake hakowa ake biyan su, zuwan Bola Tinubu an fara yunkurin mayar da hankali kan iskar gas, wanda motoci da sauran abubuwan more rayuwa ake tunanin karfafa su a bangaren iskar gas mai makon man fetur, wanda idan hakan ya faru mai mako kashe naira dubu goma akan mu'amalar man fetur, da kasa da naira dubu na iskar gas zai iya wadatarwa.
Barista Alfa, ya nemi yan Nijetiya da su jure akan wannan yanayin kowa ma yana jin shi, amma ina da kwarin guiwa a dan kankanin lokaci za mu yi murna da wadannan tsare tsaren da shugaban kasa Bola Tinubu ke kudurin aiwatarwa a kasar nan.

Sannan ina jawo hankalin gwamnatoci musamman ta jihar Neja, bisa jagorancin Manomi Umar Bago na tabbatar da dawo da martabar noma da ya tabbatar ya yi dukkan mai yiwuwa na ganin an karfafa guiwar manoma da kuma samar masu da tallafi, da kulawar da ta dace dan ganin shirin karfafa manoma miliyan daya ya tabbata.

No comments