Daga Awwal Umar Kontagora An bayyana cewar matsalolin tsaro sun fi kamari a lokacin mulkin Muhammadu Buhari fiye da wannan lokac...
Daga Awwal Umar Kontagora
An bayyana cewar matsalolin tsaro sun fi kamari a lokacin mulkin Muhammadu Buhari fiye da wannan lokacin na mulkin Bola Tinubu. Tsohon sanatan jihar Kwamred Shehu Sani ya bayyana hakan ga manema labarai, bayan kammala bukin cikar shekaru arba'in da kafa kungiyar KAGOBA na tsoffin daliban Kwalejin Kimiyya da ke Kagara a jihar Neja.
Shehu Sani ya cigaba da cewar akwai bukatar gwamnatin ta kara kaimi wajen kawo karshen matsalar tsaro a kasar nan, amma ba zai yi kasar nan ta dore a wannan turbar ba, duba da irin rawar da ilimi ke takawa amma a wayi gari wasu makarantun da suka kafa tarihi a ce a yau wadannan makarantun na gab da zama kwafai saboda barazanar hare haren yan ta'adda, wajibi shugabanni musamman a arewa su farka domin kusan manyan makarantun da mahara suka yi ta kai a hare hare a mulkin baya duk daga arewa suke.
Yanzu kamar Goverment Science Collage da ke kagara bayan kokarin rugujewa tana daya daga cikin manyan kwalejojin da suka samar da manyan farfesoshi, likitoci da jami'an tsaro da manyan yan siyasa amma yau ta zama abin tausayi sakamakon abinda ya faru da dalibanta a gwamnatin da ta gabata.
Daliban kwalejin da yanzu haka suke da sansani a Bahago Secondry School da ke cikin garin minna, sun riko gwamnatin da ta tabbatar masu da tsaro tare da gaggauta gyaran kwalejin saboda su koma Kagara dan cigaba da karatunsu a can.
An kafa kwalejin ne a shekarar 1964 a wani sashe na Bosso, a cikin karamar hukumar Bosso, sannan mayar da ita Kagara cikin karamar hukumar Rafi a shekarar 1973, a shekarar 1976 wasu dalibai daga wasu manyan makarantun sakandare suka hade a Kwalejin dan samar da kwararrun dalibai a bangaren kimiyya.
Dakta Philip Audu Bawa, shi wakilin shugaban daliban da suka kammala a shekarar 1986, wanda Kwanturola Jafaru Tukur ke jagoranta a halin yanzu, ya nuna takaicinsa kan yadda gwamnati tayi watsi da makarantar tun tsawon lokaci, ba kayan aiki ba ingantattun kayan aiki da rashin tsaron da ya kai ga baiwa yan bindiga damar shiga makarantar suka har dalibai tare da rasa ran wani dalibi, wanda a cewarsa dole ne masu ruwa da tsaki su tabbatar sun dawo da martabar kwalejin.
Sanata Shehu Sani, ya jawo hankalin tsoffin daliban da su cigaba da hada kai wajen taimakekeniya a tsakaninsu da iyalansu, wanda ko bayan ba su zumuncin karatu tare ba zai rushe ba.
Daliban da suka shirya taron, dallibai ne da suka kammala karatunsu a kwalejin a shekarar 1984,wanda yanzu kungiyar ta cika shekaru arrba'in da kafuwa, wanda tarihin kwallejin ba zai gushe ba har sai an sanya gudunmawar da ta bayar wajen kyankyashe nagartattun dalibai, wanda tsohon Sanatan jihar kaduna, Kwwared Shehu Sani na cikin su.
An dai shirya ttaron ne a makarantar sakandare na Bahago Secondry School da Minna hanyar Bosso yammacin asabar din makon nan.
Bayan ziyartar dakin kwanan dalibai dan duba halin da suke, ttsoffin daliban sun shiga aji cikin kayan makaranta dan tuna yadda suke daukar darasi, tare bin layi wajjen amsar abincin yan makaranta.
No comments