Hukumar Gudanarwar Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA) da ke jihar Katsina, ta yaba wa shugaban rukunin Jami’o’in MAAUN, Farfesa Adamu Ab...
Hukumar Gudanarwar
Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA) da ke jihar Katsina, ta yaba wa shugaban
rukunin Jami’o’in MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo bisa gudummawar motocin
daukar marasa lafiya guda biyu da mota kirar ‘Luxurious’ mai daukar mutum 60 da
ya bai wa jami’ar.
Shugaban Jami’ar,
Farfesa Ar’mayau Bichi ne ya yi wannan jinjinar a lokacin da ya jagoranci
ma’aikatan gudanarwa na Jami’ar a ziyarar godiya da suka kai wa Farfesa Gwarzo
a Kano a kwanan nan.
Farfesa Bichi wanda ya
bayyana godiyarsa ga Farfesa Gwarzo bisa gagarumin tallafin da yake bai wa
FUDMA, ya ce sun kai ziyarar ne da nufin gode wa Farfesa Gwarzo bisa wannan karamcin
da ya ce yana da matukar muhimmanci wajen bunkasa koyo da koyarwa a jami’ar.
Shugaban jami’ar har
wala yau ya yaba da irin gudummawa daban-daban na ci gaban jami’ar da Malamin yake
ba su wanda ya bayyana shi a matsayin mai taimakon jama’a, inda ya jinjina masa
na musamman bisa yadda ya ba su tallafin motocin daukar marasa lafiya guda biyu
da kuma motar bas mai daukar mutane 60.
A don haka ya yi kira
da a samar da hadin guiwa a tsakanin jami’o’in biyu tare da bayyana kyakkyawan
fata cewa wannan zumuncin zai ci gaba da kyautata alakar da ke tsakanin
jami’o’in biyu.
A yayin ziyarar godiyar,
Farfesa Bichi a madadin hukumar gudanarwa, ma’aikata da kuma daliban jami’ar FUDMA,
ya mika wa Farfesa Gwarzo takardar godiya bisa yadda yake ci gaba da bai wa
jami’ar tallafi.
A nasa jawabin, Farfesa
Gwarzo ya jaddada bukatar da yake akwai na daidaikun mutane su rika yin tasiri
mai dorewa tare da tabbatar da an ga irin nasarorin da suka kawo ko da bayan ba
su nan.
Ya jaddada kudirinsa na
inganta ilimi a Arewacin Nijeriya ta hanyar kara yawan wadanda suka kammala
karatu da kuma inganta harkar ilimi.
Farfesa Gwarzo ya kara
jaddada bukatar jami’o’i da su mai da hankali kan gina kyakkyawan suna, martaba,
tare da kuma gina kyakkyawar kimar ilimi ta yadda za a samu karbuwa da damarmaki
a fadin duniya.
Shugaban rukunin jami’o’in MAAUN wanda ya yi dogon bayani kan dabarun inganta martabar jami’o’i da kuma samar da tallafi domin gudanar da ayyukan bincike, ya bayyana muhimmancin gina suna, tare da kulla alaka da cibiyoyin ilimi na kasa da kasa, da kuma muhimmancin da yake akwai na tasirin kima ga jami’a.
A yayin da yake bayar
da shawarar samar da yanayi mai kyau ga masu ilimi domin bunkasa da kuma ba da
gudummawa ga ci gaban jami'ar, Farfesa Gwarzo ya jaddada muhimmancin jami’o’i
su samar da na su hanyoyin samun nasara, maimakon dogaro da kudaden gwamnati
kawai.
No comments