Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Wani Manomi Ya Sare Direban Tarakta Da Ke Huɗa A Gonakin Su

Daga Awwal Umar Kontagora Wani ƙaramin manomi ya sare direban taraktan da ke huɗa a gonakin su, lamarin ya biyo bayan kokawa da ...

Daga Awwal Umar Kontagora

Wani ƙaramin manomi ya sare direban taraktan da ke huɗa a gonakin su, lamarin ya biyo bayan kokawa da wasu ƙananan manoma suka yi kan yadda gwamnatin Neja ta shiga aikin noma ha'in da na'in tun kafin faɗuwar ruwan sama sosai.

Ko a kwanakin baya wasu Fulani a yankin Beji da ke ƙaramar hukumar Bosso, sun koka kan yadda gwamnatin jiha ta shiga gonakin su ta share har da itatuwan da suka shekara da shekaru ba tare da barin iyakokin gonakin na su ba, inda suka ce sun gaji gonakin ne tun kaka da kakanni, amma dare daya gwamnati ta mamaye gonakinsu ba tare da wani bayani ba.
Bincike ya nuna cewar wani karamin manomi yayi kukan kura inda ya aukawa daya daga cikin direban tataktan da ke huda inda ya sare shi. kananan manoma da dama sun koka akan lamarin.

Gwamnatin jihar Neja tasa a cigaba da yin hudar cikin gonakinsu bayan da su kayi shuka, manomin yayi amfani da adda ya sare daya daga cikin direbobin taraktocin.
Bayanai da ke fitowa daga yankin karamar hukumar  Wushishi inda lamarin ya faru na nuna cewa yanzu haka direban taraktan yana kwance a asibiti rai a hannun Allah.
A karamar hukumar Mariga ne matsalar ta fara inda wasu manoma suka ce gwamnatin ta tura aka share filayen gonakin da suka ce sun kwashe sama da shekaru hamsin suna noma.

Duk da cewar Gwamnatin tace ta fada masu cewar filin gwamnati ne kuma ta hana kowa yayi noma a ciki a bana, saboda shirin ta na dawo da martabar noma da samar da abinci a kasa manoman sun musanta bayanin hanin na gwamnatin.

Bayan wani rahoton da wakilin mu ya samu yace duk da kokawar kananan manoman masu tutiya da gonakin a matsayin gonakin su na gado, gwamnatin jiha ta shiga karamar hukumar Wushishi don cigaba da share gonakin ta, inda wani manomi wanda shukar sa tayi tsiro ya kasa jurewa, lamarin da ya kai ga ya sari daya daga cikin direbobin taraktan.
Manema labarai sun tuntubi Shugaban Karamar Hukumar, Mk Yalwa wanda ya tabbatar da lamarin amma sai.dai yace da sauki kuma an riga an samu sansanci.

Wani manomi daga karamar hukumar Bosso da ya nemi a sakaya sunan sa, yace ba wani dagaci ko hakimi a yankin su da ya zauna da su ya fada masu matsayin su a wadannan gonakin, domin saura ne da suka gada tun kakanni kuma suke noma wurin ba su taba fuskantar turjuya a wurin gwamnati ba sai a wannan lokacin.
Wani abinda ya shige mana duhu shi e yadda aka kwashe har alamomin iyakar gonakin da itatuwan da suka shuka tun shekaru da dama.

Gwamnatin Neja dai ta kudurin aniyar dawo da martabar noma inda ta sha alwashin tallafawa manoma miliyan daya tare da kafa hukumar samar da abinci a jihar mai suna NIGER FOOD,wadda za tai aiki tare da ma'aikatar noma dan cin ma wannan kudurin na gwamnatin.

A shekarun baya dai manoman sun sha fama da matsalar yan bindiga wadanda ke kutsawa gonaki suna garkuwa da manoma da kai manomar da dama yin hasarar abinda suka noma saboda tserewa da fadawa tarkon yan bindiga, wanda da daman abincin da aka noma a wasu gonakin yan bindigar suka rika iko da su, wasu kuma sun noma amma sai da suka biya diyyar gonakin ga yan bindigar, wasu kuma sun cire anfanin gonar sun sayar dan biyan kudin fansar da aka yi garkuwa da yan uwan su.

Zuwa yanzu dai da daman manoma na tsugunne ba su san makomarsu ba dan sun zama yan gudun hijira daga yankunan su.

No comments