Daga Awwal Umar Kontagora A cigaba da wasan cin kofin Umar Bago na wasan Badmiton, masu ruwa da tsaki sun gwabza dan wakiltar ka...
Daga Awwal Umar Kontagora
A cigaba da wasan cin kofin Umar Bago na wasan Badmiton, masu ruwa da tsaki sun gwabza dan wakiltar kananan hukumomin da suka.fito. Da yake tsokaci ga wakilin mu, Kwamred Garba Musa Bala Kontagora daya daga cikin manya da ya buga wasar, yace sun rungumi wannan wasar ne dan nishadi da samun kwarin guiwa ga lafiyarsu.
Wannan gasar ya taimaka gaya wajen samarwa matasa natsuwa domim kusan shi ne irinsa na farko a jihar nan, kuma da ka ga muna goyon bayan wasan mu ma tsoffin yan wasa ne amma ba mun dogara da shi ba, domin kusan bayan dan tallafin da gwamnati ke bayarwa mu kan mu muna taimakawa da wasu muhimman kayan wasa da yaran ke anfani da shi.
Yanzu gaban idanun ku matasa maza da mata hankalin su ya dawo wajen wasar nan da masu shekaru irin mu, ka ga mu a bangaren mu yana taimakawa lafiyar mu, muna samun kuzari da kwarin guiwa musamman a irin wannan lokacin da ake ciki.
Wadannan kananan hukumomin da suka halarci wannan wasar muna kyautata zaton nan gaba sune zasu zama wakilan jihar nan da kasa baki daya, saboda haka ba cin wasan ne muhimmi ba, sha'awa da sanya abin a zuciya zai taimaka matashi samun hanyar da zai nusar da kan sa wajen samun abinda zai dauke hankalin shi, ta yadda zai taimaka wajen kaucewa zaman banza da rashin abin yi.
Maganar yadda wasan ke gudana a yanzu, gaskiya yaran sun nuna da gaske suke, domin yadda wasan ke gudana kamar yadda na fahimta akwai sha'awa da son abin a zukatan su.
Wasar Badmiton wasa ne da ke cin kudi sosai, domin kayan wasan ba su da sauki amma tunda muna samun tallafi daga wasu manya da ita kan ta gwamnatin jiha, za mu cigaba da sanya idanu da tallafawa da dan abinda muke samu gurin sayen Raket da Shettle dan ganin mun cin ma burin mu na cigaban wasan Badmiton a jihar nan, domin idan ba mu taimaka masu ba ko suna son bugawa ba zasu iya bugawa ba.
Yanzu an shiga wani yanayin da idan matashi bai natsu ya samarwa kan shi madafa, za ka ga al'umma na kyamatarsa, saboda haka muna jinjinwa gwamnatin jiha da shugabannin kungiyar Badmiton na jiha bisa jagorancin basarake Hon. Mohammed Nma Kolo ( Jawon Minna, Amanan Agaie) bisa namijin kokarin shirya wannan gasar dan mun san irin abubuwan da yayi dan samun wannan nasarar da muke gani a yanzu.
No comments