Daga Awwal Umar Kontagora Ƙungiyoyin Fulani ta 'Fulani Youth Initiative Developments' tare da haɗin guiwar 'Fulani Y...
Daga Awwal Umar Kontagora
Ƙungiyoyin Fulani ta 'Fulani Youth Initiative Developments' tare da haɗin guiwar 'Fulani Youths Sai Bago Again Organisation', sun shirya gangamin wayar da kan makiyaya muhimmancin mallakar katin zabe. Tunda farko a bayaninsa sakataren kungiyar Comr. Sulaiman Ruga ya bayyana cewar ganin hukumar zabe ta tsayar da ranar fara aikinta sabunta katin zabe da tabbatar da cewar al'ummar makiyaya sun baiwa iyalansu damar mallakar katin zaben, wanda aikin kungiyoyi ne masu zaman kan su tashi tsaye wajen wayar da kan al'umma.
Sakataren ya cigaba da cewar mun fara ne da kananan hukumomin da ke nesa, yanzu mun shiga karamar hukumar Bargu, da Mokwa wanda muna da mutane da dama a wadannan wuraren.
Daga cikin abinda muka tsara, shi ne zama da sarakunan Fulani da shugabannin kungiyoyi dan cigaba da wannan muhimmin aikin, kuma mun godewa Allah bisa wannan ziyarar yau mun fahimci akwai dinbin Fulani da ke zaune a dazuka ba su mallaki katin zabe ba, balle su san anfanin shi gare su.
Ɗaya daga shugaban da muka zanta da shi, Sarkin Maganin Arewa, Amb. Dr. Abubakar Aliyu daga karamar hukumar Bargu, yace maganar gaskiya fitowar wannan kungiyar mun ji dadinsa sosai, domin mun zauna da su kuma mun ga tsare tsarensu wadanda zasu anfanar da al'ummar Fulani.
Sarkin Magani, ya cigaba da cewar ba mu taba samun wata kungiya ko gwamnati da ta shirya mana irin wannan ba, yanzu abubuwan da muke fahimta akwai mutanen da sun shige jikin gwamnati suna ci da gumin mutanen mu. Saboda haka za mu tabbatar mun marawa wannan kungiyar dari bisa dari, saboda mun ga kudurce kudurcen masu fa'ida ne.
Sarkin Fulani Dangi, daga karamar hukumar Mokwa, kuwa cewa yayi maganar katin zabe, mun san alfanunsa a lokacin zabe, amma ba mu san alfanunsa ba bayan zaɓe.
Amma tunda wannan kungiyar ta fito kuma mun ga ayyukan da ta fara na taimakawa al'ummar Fulani, za mu tabbatar mun hada karfi da karfe dan ganin al'ummar mu sun anfana.
Mun ji cewar kun dauki yaran mu suna koyon kwanfuta mai kwakwalwa, sannan sun baiwa yaran mu tallafin karatu, yau kun taso dan wayar mana da kai kan muhimmancin katin zabe.
Kamar yadda muka bada tabbacin shiga daji dan wayar da kan yan uwan mu, idan lokacin fara wannan aikin yayi ku hada mu da ma'aikatan katin zabe dan ganin an samu nasara.
Comr. Ruga, yace bayan kananan hukumomin Bargu, da Mokwa, yanzu zasu dosa Wushishi, Agwara da Rijau a yankin Neja ta arewa, sannan kuma a cikin wannan satin zasu fuskanci kananan hukumomin Suleja, Tafa da Gurara.
Kungiyar dai ta bada tabbacin cigaba da bada gudunmawa wajen wayar da kan makiyaya muhimmancin duk wani kudurin gwamnati da zai zama mai anfani ga gwamnati da al'ummar Fulani.
No comments