Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kungiyar Matasan APC Ta Yi Allah-Wadai Da Zargin Da PDP Ta Yi

Daga Awwal Umar Kontagora Kungiyar Matasan Jam’iyyar APC da kuma tuntuba ta yi Allah-wadai da jam’iyyar PDP kan zargin da ake yi wa karamin ...


Daga Awwal Umar Kontagora

Kungiyar Matasan Jam’iyyar APC da kuma tuntuba ta yi Allah-wadai da jam’iyyar PDP kan zargin da ake yi wa karamin ministan tsaro, Honarabul Bello Mohammed Matawalle da muzgunawa ‘yan adawa a yankin Arewa maso Yamma.

Shugaban kungiyar, Alhaji Ashiru Tukur, ya bayyana zargin a matsayin farfagandar siyasa mara tushe kuma arha da nufin bata sunan gwamnatin APC. Ya bukaci dattawan jam’iyyar PDP da su maida hankali wajen magance rikicin cikin gida a maimakon yin zarge-zarge marasa tushe.

Alhaji Tukur ya bayyana cewa jam’iyyar PDP tana da tarihin gazawa wajen kawo rashin zaman lafiya a siyasan ce. Ya yabawa Minista Matawalle a matsayin mai bayar da tallafi ga wadanda ambaliyar ruwa ta rutsa da su a jihar Zamfara, duk da cewa yana fuskantar tsangwama daga Jam'iyyar PDP a jihar da matakin kasa.

Kungiyar ta bukaci shugabannin PDP da su ba su uzuri cikin gaggawa kan kamfen da suka dauki nauyin yi wa Minista Matawalle da sauran shugabannin APC. Sun bukaci ‘yan Nijeriya da su yi taka-tsan-tsan da masu neman rusa maslaha saboda son kai.

No comments