Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

‘Yan Sanda sun kai hari kan masu tattakin arba’in na Imam Husaini A Abuja, sun kashe da dama

Daga Zailani Mustapha Mabiya Harkar musulunci a Nijeriya wadanda aka fi sani da 'yan shi'a sun bayyana cewa; jami'an tsaron ...


Daga Zailani Mustapha

Mabiya Harkar musulunci a Nijeriya wadanda aka fi sani da 'yan shi'a sun bayyana cewa; jami'an tsaron 'yan sandan Nijeriya sun afkawa masu tattakin arba'in na Imam Husaini a birnin Tarayya Abuja. 

Wannan sanarwar na dauke ne a wata takardar manema labarai da Sheikh Sidi Munir Mainasara Sokoto ha sanyawa hannu a madadin Harkar Musulunci a Nijeriya a karkashin Shaikh Ibraheem Zakzaky a ranar Lahadi 25 ga watan Agustan 2024. 

Takardar ta soma da cewa; "Muna so mu sanar da al’umma cewa ‘yan sanda sun kai farmaki kan tattakin Arba’een da yake gudana a Wuse a birnin Tarayya Abuja tare da kashe mutane da dama. A yayin da ake kokarin tarwatsa masu tattakin na Arbaeen, ‘yan sandan sun kashe tare da raunata masu tattakin da dama", in ji sanarwar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa; "A halin yanzu, jami'an tsaro sun shagaltu da kama masu tattakin.

"Likitoci na kula da wadanda suka samu munanan raunuka, kuma za a gabatar da cikakkun bayanai na wadanda aka kashe, da wadanda suka jikkata, da kuma wadanda aka kama ga manema labarai nan gaba kadan.

"Kafin a fara tattakin, mun binciki dukkan mahalarta taron domin tabbatar da cewa babu kutse, kuma taron zai kammala kamar yadda aka tsara.

"Tattakin Arbeen din da aka gudanar a jiya a yankin Masaka da Zuba ya kare lafiya kuma cikin nasara", sanarwar ta karkare.


No comments