Babban wakilinmu tare da shugaban jami'ar Northwest University Sokoto, Farfesa Ahmed Maigari Ibrahim suna tattaunawa. Shugaban Jami’ar N...
![]() |
Babban wakilinmu tare da shugaban jami'ar Northwest University Sokoto, Farfesa Ahmed Maigari Ibrahim suna tattaunawa. |
Shugaban Jami’ar Northwest Univesity Sakkwato, Farfesa Ahmed Maigari Ibrahim, ya bayyana cewa daga cikin nasarorin da ya samu tsawon shekaru biyu da jan ragamar jami’ar Northwest University Sakkwato, shi ne samar da kwasa-kwasai a bangaren lafiya har guda goma.
Farfesa Maigari ya bayyana hakan ne a yayin ganawarsa da manema labarai a Kano a karshen mako, inda ya ce a yanzu jami’ar tana da adadin kwasa-kwasai ashirin da bakwai da take koyarwa.
Shugaban jami’ar ya tabbatar da cewa; sakamakon himma da kwazo da ma’aikatan jami’ar suka nuna ne ya samar da wannan nasarar, “zimma da kwazo da muka samu daga ma’aikata ne ya kai ga har mun kara samun kwasa-kwasai guda goma (10). A halin yanzu dai muna kwasa-kwasai guda ashirin da bakwai”, ya tabbatar.
Ya bayyana cewa; daga cikin manya-manyan kwasa-kwasai da suke yi a jami’ar sun hada da, ilimin likitanci (MBBS), da bangaren magani (Pharmacy), da jinya (Nursing science) da ilimin kimiyyar gwaje-gwaje (Medical Laboratory Science), da ilimin tsaftar muhalli (Environmental Health), da lafiyar al’umma (Public Health).
Sannan kuma ya ci gaba da cewa; “muna kimiyyar kwamfuta (Computer Science), muna tsaron yanar gizo (Cyber Security), muna Injiniyar kwamfuta (Computer Engineering), da sauran su.
“Bangaren huldar dan adam (Humanity) muna koyar da sha’anin banki da kudi (Banking & Finance), sha’anin kudi (Accountancy), tsimi da tanadi (Economics), ilimin zamantakewa (Sociology), da ilimin halayyar dan adam (psychology).
“Bangaren tsangayar ilimin koyarwa kuwa, muna da ilimin karantar da halayyar dan adam (Educational psychology), sannan muna yin limi daga tushe (Educational Foundation), muna kuma fasahar ilimi (educational technology)”, ya jaddada.
Ya tabbatar da cewa; jami’ar ya zuwa yanzu tana da tsangayoyin ilimi har guda bakwai da suke karantar da kwasa-kwasai daban-daban. Tare da dalibai dari biyar (500), “a yanzu dai muna da tsangayoyi guda bakwai (7). Muna da yawan dalibai sun kai guda dari biyar (500).”
Ya ce yana da tabbacin a yanzu za su samu karin dalibai sosai ganin yadda suka samar da kwasa-kwasai har guda 10 a bangaren lafiya kawai; “za mu ci gaba da samun dalibai saboda idan ka duba kwasa-kwasai na bangaren lafiya har wajen guda goma (10), to wannan zai taimaka matuka gaya don samun dalibai”.
Ya ce kafa jami’ar ya samar da ci gaba ta fuskacin daukar ma’aikata da bunkasa kasuwancin al’ummar yankin.
Ya yi kira ga al’umma da su kawo ‘ya’yansu jami’ar saboda saukinta, inda ya ce; “ina kiran al’umma kan cewa a zo su ci wannan garabasa saboda makarantar an kafa ta ne a kan jigon taimako. Idan ka dubi kudin makarantar abin da muke caza, bai fi daya bisa ukun da sauran jami’o’i suke caza ba. Saboda haka ina kiran al’umma kan cewa su zo su ci wannan moriya domin a kai ga nasara”, ya tabbatar.
Ya karkare da cewa; babban burinsa shi ne jami’ar ta zama abin alfahari da koyi a Nijeriya.
No comments