Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ambaliyar Ruwa: Gwamnan Jihar Kebbi Ya Karɓi Baƙuncin Ministocin Kuɗi Da Kasafin Kuɗi

Daga Awwal Umar Kontagora Ministan kuɗin Najeriya Mista Wale Edun tareda rakiyar Ministan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arzikin Naje...



Daga Awwal Umar Kontagora

Ministan kuɗin Najeriya Mista Wale Edun tareda rakiyar Ministan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arzikin Najeriya Sanata Abubakar Atiku Bagudu CON ya kawo ziyarar jaje da gani da ido garin Birnin Kebbi a sanadiyar ambaliyar ruwa da aka samu a wasu sassan jihar ta Kebbi.

Maigirma Gwamnan Jihar Kebbi Kwamared Dakta Nasir Idris Ƙauran Gwandu ya ƙarbi baƙuncin ministocin a garin Birnin Kebbi a ranar lahadi 25/08/2024.

A lokacin ziyarar tasu, ministocin sun ziyarci shiyar Fadama dake ƙaramar hukumar mulki ta Argungu da kuma ƙaramar hukumar mulki ta Birnin Kebbi.

Haka kuma a ziyarar da ministan kuɗin yakai garin Argungu, ya samu garzayawa zuwa babban kamfanin sarrafa shinkafa na WACOT dake garin Argungu.

Da yake jawabi a lokacin ziyarar, ministan Kudi Mista Wale Edun ya bayyana cewar sunzo Jihar Kebbi ne domin gani da ido irin ɓarnar da ambaliyar ruwan tayi a jihar ta Kebbi.

Haka kuma yayi godiya ta musamman ga maigirma Gwamna Kwamared Dakta Nasir Idris Ƙauran Gwandu bisa zagayawa da yayi dasu zuwa wasu wuraren da ambaliyar ta shafa a jjhar.

Haka kuma a yayin jawabin nasa, ministan ya bayyana cewar Gwamnatin tarayya zata tallafawa dukkanin Jihohin da ambaliyar ruwan ta shafa da kuɗi Naira biliyan uku (₦3b) harda babban Birnin tarayya, Abuja domin rage raɗaɗin da ambaliyar ruwan ta haifar da kuma magance matsalolin ambaliyar ruwan musamman manoma da suka rasa gonakinsu da abincinsu.

Haka kuma ya bayyana cewar Gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinibu tana kokari sosai wajen ganin an samu tsaro a Najeriya wanda zai bayarda dama ga masu zuba jari a kasashen waje shigowa Najeriya domin saka hannun jarinsu da yadda zasu samar da aiki ga matasan yankin ta hanyar irin hannun jarin da kasashen zasu zuba. 

No comments