Daga Awwal Umar Kontagora Dalibai mata na j kwalejin horas da malamai, mallakin gwammnatin Neja da ke minna, sun yi kiran gaggawa ga hukumar...
Daga Awwal Umar Kontagora
Dalibai mata na j kwalejin horas da malamai, mallakin gwammnatin Neja da ke minna, sun yi kiran gaggawa ga hukumar kwalejini ta COE da ke Minna da ta gaggauta daukar matakai na yawaitan ganin macizai a kwalejin.
Bayanan da wakilin mu ya tattara mana sun tabbatar da cewar dalibai mata da ke kwana a kwalejin na cikin fargaba da tashin hankali sakamakon yawan ganin macizai da kuma sauro na fitar arziki a inda suke kwana.
Hakan ya samu sanadi ne daga yawan ciyawa wanda ya kamata a ce ana sanya masa maganin feshi akalla duk makonni biyu.
Wata Daliba ta shaida ma wakilin mu cewar sama da mako biyu kenen ba'a kawo masu ruwa ba, inda sai sun yi tafiya mai nesa don neman ruwan.
Dalibar da ta roki a sakaya sunan ta, ta roki cewar a kawo masu daukin gaggawa don suna cike da fargaba tare da yawan samun rashin lafiya ta zazzabin Malaria.
No comments