Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Hukumar NIWA Ta Gudanar Da Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Kan Matakan Kariya Ga Masu Amfani Da Jirgin Ruwa A Kebbi

Daga Awwal Umar Kontagora Hukumar kula da hanyoyin ruwa ta kasa (NIWA) ta shirya taron kwanaki biyu ga masu ruwa da tsaki da ke amfani da ji...

Daga Awwal Umar Kontagora

Hukumar kula da hanyoyin ruwa ta kasa (NIWA) ta shirya taron kwanaki biyu ga masu ruwa da tsaki da ke amfani da jiragen ruwa tun a ranar 24 zuwa 25 ga watan Agusta, 2024, domin magance matsalar yawan samun ambaliyar ruwa, wayar da kan masu ruwa da tsaki, da kuma fasinjojin masu shiga jirgin ruwa a matsayar wata hanyar zirga zirga ga resu a jihar Kebbi musamman mutanen da ke kusa da ruwan kogi.

Taron wanda ya samu halartar wakilai daga mai martaba Sarkin Yauri, HYPPAD, karamar hukumar Mulki ta  Yauri, hukumomin tabbatar da tsaro, taron dai mayar da hankali ne kan illolin da ke tattare da ambaliyar ruwa da kuma muhimmancin bin ka’idojin kariya yayin amfani da jiragen ruwa kuma a matsayin mutun fasinja Muhimmiyar tattaunawa ta ta'allaka ne kan matakan kariya na wajibi, dangane da Sanya riguna na rai kafin shiga kwale-kwale, Hana tafiye-tafiye da daddare, Samun na'urorin kashe gobara a cikin jirgin. Haka kuma wuce ka'idar lodin kaya ko fasinjojin don hana kifewar jirgi.

Jami'an NIWA sun jaddada cewa wadannan matakan kariya  ayyuka ne masu mahimmanci don guje wa bala'i. Hukumar ta kuma yi karin haske kan ka'idojin sufuri na baya-bayan nan da majalisar dokokin ta kafa, wanda ya ba da umarnin sanya rigar ceto ga dukkan fasinjoji kafin tashin jirgi.

An kammala taron da yin kira da a dauki matakan kariya, inda aka bukaci masu amfani da hanyoyin ruwa da su dauki nauyin kare lafiyarsu da sauran su. Hukumar NIWA ta nanata mahimmancin aiwatar da wadannan ka'idoji don kare afkuwar asarar rayuka, musamman a lokacin damina. 


No comments