Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Jihohin Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa Da Naira Biliyan Uku–Inji Ministan Kudi Wale Edu

Daga Awwal Umar Kontagora Gwamnatin tarayya ta amince da Naira biliyan uku domin tallafawa jihar Kebbi da sauran jihohin da ambaliyar ruwa t...



Daga Awwal Umar Kontagora

Gwamnatin tarayya ta amince da Naira biliyan uku domin tallafawa jihar Kebbi da sauran jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa ciki har da babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda ministan kudi Wale Edun ya sanar a Birnin Kebbi yayin wata ziyarar aiki da ya kawo ta kwana daya a jihar.

Edun, wanda ya duba gonakin shinkafa da ambaliyar ruwa ta shafa a Argungu, ya bayyana cewa, majalisar zartawa da tattalin arzikin kasa (NEC) ta amince da kuma mai da hankali wajen tallafa wa jihohi da babban birnin tarayya da naira biliyan uku domin dakile illolin ambaliyar ruwa da kuma bunkasa noman abinci.

Majalisar zartawa ta tarayya ta amince da fitar da kudaden don tallafa wa manoman da suka yi asarar amfanin gona a sanadin ambaliyar ruwa, inji Edun. Ya bayyana jin dadinsa da yadda kungiyar  kamfanin Shinkafar  Wacot ke gudanar da ayyukan da kuma samar da aikin yi ga matasa a jihar Kebbi, inda ya ce ta samar da dubunnan ayyukan yi da kuma yadda za ta ciyar da daukacin al’ummar kasar nan da abincin da suka dace.

Mista Edun ya kara da cewa, shugaba Tinubu na son taimakawa wajen fadada masana’antar shinkafa da sauran kananan masakun shinkafa a jihar Kebbi domin bunkasa noman abinci, rage hauhawar farashin abinci, da samar da ayyukan yi.

Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ya yi kira ga Shugaba Tinubu da ya tallafa wa manoman shinkafa da ambaliyar ruwa ta shafa, inda ya bayyana cewa jihar Kebbi za ta iya ciyar da al’umma da tallafin da ya dace.

Gwamnatin jihar dai ta samar da takin zamani, injinan fanfon ban ruwa kyauta ga manoma da shirin yin noman rani mai yawa.

Ministan kasafin kudi da tsare-tsare na tattalin arziki Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya yabawa jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wajen gyara tattalin arzikin kasar sannan ya bayyana cewa ayyukan titin Sokoto zuwa Badagary a Legas zai taimakawa manoma wajen noman damana da samar da abinci. 

No comments