Daga Awwal Umar Kontagora Gwamnatin Jihar Kebbi ta raba naira Blbiliyan 6.5 ga mutane 65,000 a kananan hukumomi 21 na jihar Kebbi da suka c...
Daga Awwal Umar Kontagora
Gwamnatin Jihar Kebbi ta raba naira Blbiliyan 6.5 ga mutane 65,000 a kananan hukumomi 21 na jihar Kebbi da suka ci gajiyar shirin a karkashin shirin ba da tallafi na ‘Kaura Cares’. Gwamna Nasir Idris ne ya kaddamar da shirin rabon kudaden a Birnin Kebbi, ya bayyana cewar kowane mutun guda zai ci gajiyar tallafin na Naira 100,000.
A wata takardar manema labarai da sakataren yada labaran gwamnan, Malam Ahmad Idtis ya fitar yammacin littinin din makon nan, ya bayyana cewar ba a taba baiwa manoma irin wannan tallafin a jihar ba. Yace gwamna Nasiru Kaura, ya bayyana cewar shirin na da cikin alkawurran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe, kuma ya rubanya wadanda suka fara cin gajiyar shirin har sau hudu. Ya kuma umurci ma’aikatar lafiya ta jihar da ta zakulo masu bukatar ta rashin lafiya da ke jinya, wanda jihar za ta dauki nauyin biyan kudaden kulawa da lafiyarsu don gwamnati na ganin cewar ya kamata ta dauki nauyin biyan kudaden masara lafiya da ba su da karfi.
Kwamishinan Ma'aikatar Kasafin Kudi da tsare tattalin arzikin jihar Kebbi, Dakta Abba Sani Kalgo, ya bayyana cewar gwamna ya amince da fitar da zunzurutun kudi har Naira biliyan 6.5 don tallafa wa mutane 65,000 na kananan hukumomi 21 na jihar dan amfana da kuma samun gudanar sana'o'in dogaro da kai.
Ana jawabin shugabar shirin Kaura Care, Dokta Rukayya Muhammad Bawa, ta bayyana cewar manufofin shirin da nasarorin da aka samu a wajen taron bikin kaddamar rabon tallafin kudaden ta biyo bayan irin kudurin gwamna na inganta rayuwar al'ummar jihar ne, musamman bangaren noma da kiwon lafiya.
No comments