Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Zaben Kananan Hukumomi: Jam'iyyar APC Na Yawuri Ta Kaddamar Gangamin Yakin Neman Zabe

Daga Sani Twoeffect Yawuri Kwamitin gangamin yakin neman zaben a karkashin jagorancin Kwamishinan sufuri da makamashi Honorabul Bala Gagga t...



Daga Sani Twoeffect Yawuri

Kwamitin gangamin yakin neman zaben a karkashin jagorancin Kwamishinan sufuri da makamashi Honorabul Bala Gagga tare da sauran yan kwamitin sa, sun kaddamar da gangamin yakin neman a gundumomin Chulukoma/Gumbi, Jijima da zamare yau litinin 26/8/2024.

Tun a farko dai kwamitin gangamin yakin neman ya isa gidan Uban Kasar zamare domin neman tubarraki, inda basaraken yayi musu Addu'ar fatan Alheri, tare da yabo ga gwamnatin maigirma Gwamnan jihar Kebbi Kwamared Dr Nasir Idris Kauran Gwandu akan irin ayukkan Alheri daya gudanarwa.

Hakama gangamin yakin neman zaben ya samu manya manyan yan siyasar Kasar Yawuri da suka hada da; Dan majaisar jiha mai wakiltar Yawuri, honorabul Hashimu hinan biro, Shugaban jam'iyyar Apc Yawuri Yusuf Alhassan  Alhaji Zaki mental, Alhaji Garba Bakanike, malam Lukman Yelwa, honorabul Yusuf Sani rukubalo, honorabul Aminu Gumbi, Abdullahi zamare, Alhaji Alh Bala Jihab Yauri  da dai sauran su.

Daga Karshe kwamitin ya gabatar da Dan takarar Shugaban karamar hukumar mulki ta Yawuri honorabul Abubakar shuaibu tare da kansilolin wadannan mazabun guda uku. 

No comments