Daga Idris Umar, Zariya Mahaifin Aisha Musa Auyo, Darakta, Neptune Prime Network, ya rasu. Farfesa Musa Abdu Auyo, ya rasu yan...
Daga Idris Umar, Zariya
Mahaifin Aisha Musa Auyo, Darakta, Neptune Prime Network, ya rasu. Farfesa Musa Abdu Auyo, ya rasu yana da shekaru 63. Farfesa Auyo ya rasu da sanyin safiyar ranar Talata, 27 ga watan Agusta a gidansa dake rukunin gidajen ma’aikata na Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK quarters).
Za a yi jana’izarsa a yau Talata bayan Sallar Azahar da misalin Æ™arfe 1:00 na rana a Masallacin Juma’a na BUK.
Kafin rasuwarsa, Farfesa Auyo yana aiki da sashen Laburare da Kimiyyar Watsa Labarai na Jami’ar Bayero Kano (BUK). Ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya tara da kuma jikoki tara. Daga cikin ‘ya’yansa akwai Misis Aisha Musa Auyo, Darakta na Neptune Prime.
Shugaba kuma mawallafin jaridar Neptune Prime (Publisher/CEO) Dakta Hassan Gimba, da É—aukacin ma’aikatan Neptune Prime Network suna miÆ™a saÆ™on ta’aziyya ga Aisha Musa Auyo da sauran iyalan mamacin da kuma al’ummar BUK bisa ga wannan babban rashi.
Allah ya jiƙansa da rahama ya sa Jannatul Firdausi ce makoma.
No comments