Daga Awwal Umar Kontagora A kokarin da gwamnatin Neja ke yi na daidaita lamurran tsaro a jihar, wani sabon rikicin da ya taso a ...
Daga Awwal Umar Kontagora
A kokarin da gwamnatin Neja ke yi na daidaita lamurran tsaro a jihar, wani sabon rikicin da ya taso a ƙauyen Barkuta da ke yankin Beji na ƙaramar hukumar Bosso a Talatar makon nan bayan tsintar gawar wani manomi da aka kashe kuma aka ɗora adda a gawarsa, ya janyo rasa rayukan mutum biyar sakamakon ɗaukar fansar da 'yan uwan mamacin suka yi na aukawa makiyayan da ke zaune a yankin.
Kamar yadda rahotanni suka tabbatar a safiyar talatar nan ne aka tashi cikin tashin hankali a kauyen Barkutu sanadiyyar rikici tsakanin manoma da makiyaya, wanda yan uwan mamacin suka nuna fushin su da ɗaukar fansa akan waɗanda ba su san da abin da ya faru ba.
Da take tabbatar da faruwar lamarin, shugabar ƙaramar hukumar Bosso, Hajiya Ladidi Bawa Bosso ta ce yanzu haka bayan faruwar lamarin, komai ya lafa kuma jami'an tsaro suna kan lamarin gadan-gadan.
Shugaban ta tabbatar da cewa wasu makiyaya ne suka hallaka manomin har lahira a gonar sa, wanda hakan ya janyo rikicin.
Ta ce za su gudanar da bincike kuma duk wanda aka kama da hannu zai dan'dana kudar sa.
Gwamnatin Neja, ta sha alwashin kawo ƙarshen ire-iren wadannan rikice rikicen na manoma da makiyaya, wanda ta kai ga samar da ma'aikatar kula jin daɗin manoma da makiyaya, dan sauraren ƙorafe ƙorafen yanayin da ke tasowa.
A wani hirar da wakilin mu ya taɓa yi da kwamishinan ma'aikatar kula da jin daɗin manoma da makiyaya, Hon. Umar Sanda Rabe, ya ce ma'aikatarsa na aiki kafaɗa da kafaɗa da ma'aikatar kula da harkar noma, sun kafa kwamitoci daban daban da za su riƙa bibiya da sauraren korafe korafe wanda gwamnati ta sanya kafar wando daya ga duk wanda bai son zaman lafiya.
Ya ce babban manomin jiha, Umar Mohammed Bago ya samar da dukkan abubuwan da ake bukata, wanda jami'an tsaro da gwamnati na aiki kafada da kafada dan tsare rayuka da dukiyoyin jama'a.
Saboda ba dalilin da zai sa mutane su riƙa aikin rashin hankali na tada hankali da kashe kashen rayuka da ɓarnata dukiyoyi.
No comments