Daga Awwal Umar Kontagora An yi kira ga Fulani da Gwarawan jihar Neja da su ajiye bambancin da ke tsakaninsu da su zauna lafiya,...
Daga Awwal Umar Kontagora
An yi kira ga Fulani da Gwarawan jihar Neja da su ajiye bambancin da ke tsakaninsu da su zauna lafiya, domin su 'yan uwan juna ne kuma ba yadda za su cigaba muddin suna bai wa shaiɗanu kafa a tsakanin su.
Hajiya Aisha Mohammed (Maman Khalid) wata Dattijiyar ƴar siyasa ce ta yi kiran jim kaɗan da samun hargitsi tsakanin Fulani da Gwarawa a garin Beji ta ƙaramar hukumar Bosso da ya kai ga salwantar rayuka talatar makon nan.
Maman Khalid, ta cigaba da cewar, "mu a hannun gwarawa muka yi rayuwa kuma akwai amana a tsakanin mu da juna, amma yau abin baƙin ciki wasu ɓata gari suna ƙoƙarin hargitsa wannan zumunci ta hanyar kunna wutar rikici a tsakanin mu wanda wannan ba daidai ba ne", in ji ta.
Ta ƙara da cewa; "Ya kamata dukkanin ɓangarorin biyu su yi karatun ta natsu, su fahimci wannan turbar da suka ɗauka ba mai ɓullewa ba ne, domin rikici bai kawo cigaba illa ya haddasa gaba da ƙiyayya, wanda hakan koma baya ne ga zaman lafiya".
Ta ce babban manomi gwamna Umaru Mohamned Bago, ya janyo kowa a jika ba maganar hassada ko bakin ciki ga juna, saboda haka idan har da gaske muna son cigaban jihar nan da mu kan mu wajibi ne ajiye makamai mu rungumi zaman lafiya, domin ba wanda ya isa ya tada wani a jihar nan, domin dukkanin mu muna da hakki, iyaye da kakanni da mu kan mu a nan muke rayuwa, kuma kasa ba ta cigaba muddin ba zaman lafiya.
Da ta juya kan muradun gwamnatin jiha kuwa, ta nemi babban manomin jiha, Umar Bago da ya samar da matsugunni na dindin din ga matan fulani dan cigaba da kasuwancin su na yau da kullun, domin yawon talla bai haifar da da mai ido ga ya mace.
Ya kamata dukkanin shiraruwan gwamnati na koyar da sana'o'in hannu a rika sanya matan fulani a ciki domin mun shiga lungu da sako wajen tallata gwamnatin nan a lokacin zabe, amma duk lokacin da gwamnati ta shirya horar da mata, mu fulani sai dai mu ji a shanun talla, wanda ya kamata ma'aikatar kula da jin dadin manoma da makiyaya tayi wani abu akai a daina barin matan fulani a baya.
Mun ji cewar gwamnati na da kudurin samar da wani dubara na bin rugage dan sanyi madara a hannun matan fulani, ya kamata idan an samu nasarar wannan kudurin, dan inganta rayuwar matan fulani a samar masu sana'ar cikin gida zai kawar da tunanin su na yawaitan shigowa gari dan wata bukatar da ba ta taka kara ya karya ba.
Maman Khalid, tace mun ji gwamnati ta bada mukaman siyasa, amma mu da muka shige sahin gaba a lokacin yakin neman zabe har yanzu ba a tuna da gudunmawar da muka bayar ba.
Yanzu haka, a kullun ina samun baki daga rugage dan jin halin da gwamnati ke ciki, mun samu ma'aikata, mun samu kwamishina amma mu mata an bar mu a baya, mu kan mu muna da gudunmawar da za mu bayar wajen tattausa zukatan matan fulani, ya kamata a dubi korafin mu.
Yar siyasar ta yabawa shugabanni da sarakunan fulani wajen bada gudunmawar su na fadakar da al'ummar fulani musamman wajen hadin kai da zaman lafiya, wanda hakan ya taimaka gaya wajen samun nasarorin da ake gani yanzu.
Ta ce, mata su san da sanin duk wani bata gari da zai yi anfani da su wajen tada hargitsi rayuwarsu ce ya ke batawa, ya zama wajibi iyaye su baiwa yayansu ilmin addini da na zamani domin su ne gishirin rayuwa, ba a rayuwa cikin jahilci ayi nasara, ba a samun cigaba da jahilci, duk wanda ya inganta rayuwar yau, gobensa za tai kyau, in ji ta.
No comments