Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnan Kebbi ya sha alwashin gyara wasu hanyoyi da gadoji da ruwa ya lalata a ƙananan hukumomin Suru da Maiyama

Daga Awwal Umar Kontagora Gwamnan ya sha alwashin gyara hanyoyin Suru da Maiyama da ruwan sama yayi sanadiyar lalacewar su, gwamnan ya bayya...


Daga Awwal Umar Kontagora

Gwamnan ya sha alwashin gyara hanyoyin Suru da Maiyama da ruwan sama yayi sanadiyar lalacewar su, gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyarar gani da ido da ya kai kan hanyar Suru zuwa Kawara da Ɗakingari da kuma wasu gonakin shinkafa da ambaliyar ruwan sama ya lalata.

Da yake jawabi a lokacin ziyarar, Gwamna Nasiru Kauran Gwandu ya bayyana cewar gwamnatinsa a shirye take ta taimakawa dukkanin al'ummar jihar musamman waɗanda suka samu jarabawa irin wannan.

Saboda haka gwamnati za ta gyara hanyoyin da gadojin da ambaliyar ruwan ya lalata a ƙananan hukumomin na Suru da Maiyama kuma gwamnatin za ta cigaba da tallafawa manoma a faɗin jihar Kebbi baki ɗaya.

Haka kuma ya bayyana cewar gwamnatinsa za tayi dukkanin abinda za ta iya wajen tabbatar da an samu wadataccen abinci a jihar Kebbi.

Suma da suke jawabi a wurin, fan Majalisar dokokin mai wakiltar ƙaramar hukumar Suru, Hon. Faruku Maisudan da Ɗan takarar kujerar shugabancin ƙaramar hukumar mulki Suru karkashin jam'iyyar APC Mohammed Lawal da kuma hakimin Kawara dukkaninsu sun yabawa Maigirma gwamna bisa irin kokarin da ya keyi wajen taimakawa manoman jihar Kebbi da kayan aikin noma.

Haka kuma gwamnan ya kai ziyarar gani da ido na barnar da ambaliyar ruwan tayi akan hanyar Jega zuwa garin Mayalo da ke ƙaramar hukumar mulki ta Maiyama.

A lokacin ziyarar, Hakimin Mayalo, Malam Abubakar Marafa. ya zagaya da maigirma Gwamna wurare daban-daban inda Maigirma gwamna yayi alƙawarin cewar gwamnati za ta gyara gadojin da ruwa ya lalata a yankin.

Haka kuma yayi musu alƙawarin cewar gwamnatinsa za tayi dukkanin abinda za ta iya wajen taimakawa manoman jihar Kebbi.

Gwamna ya kai irin wannan ziyarar gani da ido kan hanyar Diggi inda ambaliyar ruwan sama ya lalata hanyoyin ruwa inda Hakimin garin Diggi, Alhaji Abubakar Atiku Diggi ya fadawa  gwamna cewar ambaliyar ruwan sama da aka samu ne ya lalata hanyoyin ruwan.

Da yake jawabi a wurin, gwamna yayi alƙawarin cewar zai gyara hanyoyin ruwan da suka lalace.

Daga cikin tawagar gwamna a lokacin ziyarar akwai mataimakin gwamna Sanata Umar Abubakar Tafida, sakataren gwamnatin jiha, Alhaji Yakubu Bala Tafidan Yawuri, tsohon gwamnan  Kebbi Alhaji Sa'idu Usman Nasamu Dakingari, shugaban ma'aikatan jiha, Alhaji Safiyanu Garba Bena, da wasu Kwamishinoni, yan majalisu da dai sauransu. 

No comments