Daga Awwal Umar Kontagora An yi kira ga bangarorin manoma da makiyaya da su kai zuciyarsu nesa, su rungumi zaman lafiya, shi zai kawo masu y...
Daga Awwal Umar Kontagora
An yi kira ga bangarorin manoma da makiyaya da su kai zuciyarsu nesa, su rungumi zaman lafiya, shi zai kawo masu yalwar arziki. Wakilin fulanin minna kuma shugaban kungiyar Bago Ruga-Ruga ta jihar Neja, Alhaji Hassan Usman Shiroro ne ya yi kiran jim kadan janazar dan sa Muhammad Baba ya rikicin ya rutsa da shi akan hanyarsa ta zuwa Kontagora daga Minna.
Marigayi Muhammad Baba shi ne shugaban kamfanin sarrafa shinkafa ta Alhaji Hassan Shiroro, yana kan hanyarsa cikin motar kasuwa inda wasu hasalallu suke tare motocin haya da ke kan tafiya, inda suka fito da shi cikin motar suka kashe shi nan take sakamakon wani rikicin da ya barke sakamakon samun gawar wani manomin da aka tsinci gawarsa a gonarsa.
Rikicin ya lakume rayukan mutane shida, yarinya daya da wasu yan uwan juna su uku da aka iske su har rugarsu aka kashe su, da wani dattijon bafulatani da bai gani da kuma marigayi Muhammad Baba, wanda da ne ga Alhaji Hassan Shiroro mai kamfanin sarrafa shinkafa da ke minna.
Wakilin fulanin, yace wasu batagari ne da ke yiwa zaman lafiya zagon kasa, wanda gwamnatin jiha tuni ta kamo hanyar samar da maslaha ga manoma da makiyayan jihar.
Saboda ya kamata dukkanin bangarori su yi hakuri a rungumi zaman lafiya. Ya kara da cewar jami'an tsaro na bakin kokarin su, dan haka a barsu su yi aikinsu.
No comments