Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Hukumar Kare Hakkin Musulmi Ta Duniya, IHRC Ta Damu Matuka Game Da Makomar Masu Tatttakin Da 'Yan Sanda Suka Harbe

Daga Zailani Mustapha Hukumar kare hakkkin musulmi ta duniya, wato IHRC ta damu matuka game da makomar masu tattakin arba’in da 'yan s...


Daga Zailani Mustapha

Hukumar kare hakkkin musulmi ta duniya, wato IHRC ta damu matuka game da makomar masu tattakin arba’in da 'yan sanda suka kai wa hari ko kuma suka kama su a Nijeriya a yayin da suke halartar tattakin Arba'in a babban birnin tarayya Abuja.

'Yan sanda sun bude wuta kan masu tattakin a ranar Lahadi 25 ga Maris 2024 ba tare da gargadi ko an tsokane su ba a yayin da ake gudanar da tattakin cikin lumana domin nuna alhinin kan kisan kiyashin da aka yi wa jikan Manzon Allah, Imam Husayn.

Yanzu haka dai an tabbatar da cewa ‘yan sanda sun kashe masu tattakin guda hudu tare da kai gawarwakinsu zuwa wani wuri da ba a bayyana ba. Wasu daruruwa kuma sun samu raunuka ciki har da masu harbin bindiga tare da kama wasu daga cikin masu raunin a inda aka yi tattakin da kuma wani muhalli da ‘yan sanda suka dira. Har ila yau, ba a san inda suka kai su ba.

Kwashe su da ‘yan sanda suka yi wani lamari ne da ke da matukar tayar da hankali duba da irin yadda ‘yan sandan Nijeriya ke dira kan mahalarta tattakin Arba’in a matakin kisan kai.  A yayin gudanar da tarukan na Arba’in a shekarar 2019 ‘yan sanda sun kwashe gawarwakin wasu masu tattaki guda shida wadanda suka bindige har lahira, inda suka boye su domin boye laifin kisan kan da suka yi. Sai a bana ne aka saki wadancan gawarwakin bayan doguwar shari'a da aka kwashe ana gudanarwa.

Tsaron wadanda aka kama al’amari ne mai matukar damuwa da tayar da hankali. Domin a shekarar 2019, 'yan sanda sun kama wasu masu tattaki da suka jikkata daga wani asibiti da suke karbar magani. Daga baya wasu sun mutu a hannun ‘yan sanda.

Wasu rahotannin a faifan bidiyo, sun kuma bayyana cewa ‘yan sandan Nijeriya sun cire wa mata musulmi hijabi da karfi da yaji. An yada hoton bidiyon lamarin a shafukan sada zumunta. Hakan dai ya janyo cece-kuce a tsakanin musulmin kasar baki daya.

Tattakin Arba’in da ake yi duk shekara ya zama lamari da jami’an tsaron Nijeriya a ‘yan shekarun nan da suke kai mata hari, inda ba a wuce shekara guda ba ke nan, ‘yan sanda suka kai hari kan masu tattakin, lamarin da ya janyo hasarar rayuka.

An shafe shekaru 40 ana gudanar da Muzaharar Arba'in da Ashura a duk fadin Nijeriya amma a 'yan kwanakin nan an fuskanci munanan hare-hare yayin da gwamnati ta dauki matakin murkushe Harkar Musulunci ta Nijeriya da jagoranta da ke shirya irin wannan tattakin.

 

No comments