Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Anka Ya Yaba Da Yaki Da Ta'addanci Da Gwamnatin Tarayya Ke Yi A Zamfara

Daga Hussaini Yero  Tsohon mataimakin gwamnan Zamfara, Muntari Anka ya yabawa yakin da shugaba Tinubu yake yi da ‘yan bindiga, ya kuma garga...


Daga Hussaini Yero 

Tsohon mataimakin gwamnan Zamfara, Muntari Anka ya yabawa yakin da shugaba Tinubu yake yi da ‘yan bindiga, ya kuma gargadi Gwamna Dauda kan da Yaba karamin ministan tsaro Matawalle goyan baya a wajan yaki da 'yan Bindiga. 

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Muntari Ahmad Anka ya bi sahun magoya bayan gwamnatin tarayya da ma'aikatar tsaro karkashin karimin minista Bello Matawale akan yakin da ake yi da ‘yan bindiga a jihohin arewa maso yammacin kasar nan.

Kuma ya yi kira ga gwamna Dauda Lawal da karda ya kawoma shirin cikas a jihar ta Zamfara.

Hakan na kunshe ne a cikin wata takardar manema labarai da tsohon mataimakin gwamnan ya sanyawa hannu, ga manaima labarai a Gusau.

Anka wanda ya rike mukamin mataimakin gwamna a Zamfara shekara shekarar 2007 zuwa 2011.

A yayin da yake yabawa matakin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dauka na umurtar karamin ministan tsaro,Bello Matawalle da ya kai farmaki sansanin ‘yan bindiga a duk fadin yankin, jagoran ya kuma gargadi Dauda Lawal, gwamnan jihar a halin yanzu kan yadda yake tsoma baki a akan yaki da Yan Bindiga a yanzu haka.

Ya kara da cewa, wannan lamari ne da ya shafi tsaron kasa da kuma yadda sojoji ke tafiyar da su yadda ya kamata a yankin.

“Bukatar al’ummar Zamfara su mayar da hankali wajen yaki da ‘yan bindiga a halin yanzu, ba za a iya misalta shi ba, domin kamar yadda gwamnatin tarayya ke yin iyakacin kokarinta wajen ganin an samar da dawwamammen zaman lafiya a jiharmu da yankinmu, a matsayinmu na al’umma, mu ma ya kamata mu fito fili.mu ya yabawa gwamnatin tarayya ta hanyar gwamnatin jihar kan ta'asar da aka yi wa 'yan fashin.

"Wannan ba lokacin fadan siyasa bane, wata dama ce ta kawo mana a matsayinmu na shugabanni domin mu amsa kiraye-kirayen jama'ar mu na hada hannu da gwamnatin tarayya domin ganin an kawar da 'yan Bindiga gaba daya daga jihar mu da yankin mu."

Ya bayyana hakan a matsayin wani abu mai kyau kuma alama ce ta nasara cewa tsohon gwamna Matawalle a yanzu ya zama Minista a ma’aikatar tsaro ta kasa kuma ba zato ba tsammani shi ne ke gudanar da wannan aiki, inda ya bukaci ‘yan kasar da su ba shi cikakken goyon baya don samun nasara yadda ya kamata".

"Ya kara da cewa gwamnatin Tinubu za ta yi iya bakin kokarinta wajen farfado da fata zaman lafiya ga jama’a idan aka kawar da wadannan miyagu lallai mutane za su rika tafiya cikin walwala, su je gona, su samar da isasshen abinci da samar da yanayi mai kyau na ci gaba. da cigaban alumma.

No comments