Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnan Kebbi ya yi wa al'ummar jihar Borno jajen Iftila'in ambaliyar ruwa da ta afkawa babban birnin jihar

Daga Awwal Umar Kontagora Gwamnan jihar Kebbi Kwamare Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu yayi jaje ga al'ummar Maidugurin jihar Barno da if...



Daga Awwal Umar Kontagora

Gwamnan jihar Kebbi Kwamare Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu yayi jaje ga al'ummar Maidugurin jihar Barno da iftila'in ambaliyar ruwa ya shafe su, gwamnan yayi jajen ne bayan da ya je Maiduguri babban birnin jihar Borno ranar Alhamis domin yin jaje ga al'ummar jihar bisa iblftila'in ambaliyar ruwa da ta afkawa babban birnin jihar  da kuma Æ™aramar hukumar mulki ta Jere da ke kusa da babban birnin jihar.

A yayin ziyarar jajen, gwamna Nasir Idris Ƙauran Gwandu ya jagoranci wata babbar tawaga daga jihar Kebbi domin gabatar da jajen ga al'ummar jihar ta Borno inda ambaliyar ruwa ya haddasa rasa dukiyoyi da rayuwar al'umma da dama har ma da gonaki.

A lokacin da yake jawabi a ziyarar jajen, Dakta Nasir Idris Ƙauran Gwandu, ya bayyana wannan ambaliyar ruwan a matsayin ɗaya daga cikin ambaliyar ruwa mafi muni a tarihin ƙasar nan.

Haka kuma yayi kira ga gwamnan Borno Farfesa Babagana Umara Zulum da al'ummar  Borno da su É—auki wannan iftila'in daga Allah ne inda ya bayyana cewar jihar Kebbi ma ta fuskanci kusan irin wannan a shekarun da suka gabata.

Haka kuma, Ƙauran Gwandu ya tausayawa al'ummar Borno bisa irin rashin muhalli, dukiyoyi, rayuka da asibitoci, makarantu da wuraren ibada dama rayuwar al'umma da dama.

Gwamnan yayi addu'a Allah ya gafarta ma waÉ—anda suka rasu tare da addu'ar Allah ya kare faruwar hakan a gaba.

A lokacin ziyarar jajen ta maigirma gwamnan, ya samu rakiyar sakataren gwamnatin Kebbi, Alhaji Yakubu Bala Tafidan Yawuri, shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jiha, Barista Attahiru MacciÉ—o, Kwamishinan Æ™ananan hukumomi da masarautun jihar Kebbi, Alhaji Garba Umar Abubakar Dutsinmari, Kwamishinan harkokin noma, Alhaji Shehu Muazu. Sai Kwamishinan shari'a kuma babban lauyan gwamnatin jihar, Dakta Junaidu Bello Junaid Marshall, da akawun jihar Kebbi l, Alhaji Ibrahim NahaliÆ™u, da  Permanent Secretary protocol affairs, Muhammad Sagir da kuma shugaban kwalejin kimiyya da fasaha ta gwamnatin tarayya, (Waziri Umaru Federal Polytechnic) da ke  Birnin Kebbi, Dakta Usman Tunga.

A nasa jawabin, a lokacin ziyarar, gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya nuna jin daÉ—insa bisa wannan ziyarar jajen da  gwamnatin jihar Kebbi, ta kawo masa da Æ´an tawagarta da kuma irin nuna damuwa da suka yi bisa halin da al'ummar jihar suka shiga.

Haka kuma ya bayyana cewar wannan ziyarar tana nuni da irin kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin al'ummar jahohin biyu.

Muna addu'ar Allah ya kare faruwar wannan a gaba kuma ya mayarwa dukkanin waÉ—anda suka rasa dukiyoyi da mafi alheri, waÉ—anda suka rasu Allah ya gafarta musu baki daya.



No comments