Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE
Tuesday, July 15

Pages

Labarai:

Kamfanin GB Food ta karrama gwamnan Kebbi

Daga Awwal Umar Kontagora

Kamfanin GB Foods ta karrama gwamnan jihar Kebbi Kwamared Dakta Nasir Idris Ƙauran Gwandu bisa irin namijin kokarin da ya ke yi wajen bunƙasa harkokin noma a jihar.

Karramawar ta zo ne a lokacin wani babban taro da kamfanin ya gudanar a garin Trujillo da ke ƙasar Spain.
Kamfanin tace, ta baiwa gwamnan wannan kyautar karramawar ne bisa irin gudunmawar da ya ke bayarwa wajen bunÆ™asa harkokin noma da kuma samar da hanyoyin sauÆ™in kasuwanci a É“angaren harkokin gona a jiharsa. 

Da yake tsokaci kan karramawar a wurin taron, gwamna Kwamared Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu ya jinjinawa kamfanin bisa irin yadda ya samar da wani ingantaccen tsari da gudanar harkokin kasuwanci a ɓangaren harkokin noma da kuma sarrafa kayan gona.

Haka kuma gwamnan yayi fatar kamfanin yayi hulɗa da manoman jihar Kebbi wajen noman tumatir kamar yadda yake gudanarwa a ƙasar Spain inda ake samun haɗin guiwa tsakanin kamfanin da ƙananan manoma.

Haka kuma, gwamnan ya roƙi kamfanin da ya taimaka wajen samarwa da manoman na jiharsa da sabon irin masara da kuma sabuwar dabarar noman masara da shinkafa da ake gudanarwa a ƙasar Spain wanda zai baiwa manoma damar samun ton 12 zuwa 18 na masara da shinkafa a kowace hekta ɗaya.

Gwamnan ya bayyana cewar idan aka samu wannan irin da sabuwar dabarar noman zai samar da sauyi mai inganci daga samun ton 2.5 zuwa ton 3 da manoma ke samarwa a halin yanzu a kowace hekta É—aya.

Gwamna ya nuna jin daÉ—insa bisa karramawar da kamfanin yayi masa inda ya bayyana cewar hakan zai ba shi damar koyon wasu ilmomi daga kamfanin.
Daga karshe yayi kira ga kamfanin da ya haÉ—a hannu da gwamnatin jihar Kebbi wajen samar da sabbin dabarun noma ga manoman jihar wanda hakan zai bada damar manoman jihar su inganta yawan abincin da suke samarwa da kuma samar da isasshen abinci a fadin Jihar.

Shi ma shugaban kamfanin, Mista Vincenc da yake jawabi a wurin taron ya yabawa gwamna bisa irin ƙoƙarin da ya keyi wajen inganta harkokin noma da samar da yanayin kasuwanci a bangaren harkokin noma mai kyau a fadin jihar inda yace yana fatar haɗakar tasu za ta taimaka sosai wajen inganta harkokin noma da samar da wadataccen abinci da kuma inganta rayuwar al'ummar jihar Kebbi.

A lokacin ziyarar ta gwamna zuwa ƙasar ta Spain, ya samu rakiyar manyan jami'an gwamnati da suka haɗa da: sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Yakubu Bala Tafidan Yawuri, Kwamishinan harkokin noma, Hon. Shehu Muazu, sai Kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arzikin jihar, Dakta Abba Sani Kalgo, da babban lauyan gwamnatin jiha kuma Kwamishinan harkokin shari'a Dakta Junaidu Bello Marshal, da kwamishinan kuɗi Hon. Abubakar Chika da kuma babban akawun jihar, Alhaji Bello Ibrahim Nahaliƙu.

No comments