Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Maulidi: Garin Da Suke Fama Da Matsalar Tsaro Su Maida Shi Da Rana Ko Su Ciyar Da Mabukata - Khalifa Ali Sa'idu Funtuwa

Daga Hussaini Yero, Funtua Khalifan Tijaniya a Funtuwa, Aliyu Sa'idu Alti ya bayyana cewa, duk garuruwan da ke fama da matsalar tsaro a ...

Daga Hussaini Yero, Funtua

Khalifan Tijaniya a Funtuwa, Aliyu Sa'idu Alti ya bayyana cewa, duk garuruwan da ke fama da matsalar tsaro a yankunan su da su maida zaman maulidin da su ke yi na dare da rana idan kuma hakan ba za ta yiwu ba, abin da suka tara na maulidin su ciyar da al'umma mabukata albarkacin Haihuwar Manzan (SAW) shi ne ma babban maulidin a wannan lokacin da muke ciki.

Khalifa ya bayyana haka ne a lokacin jawabin fara zagayen gari na Maulidin Annabi (saw) a karamar Hukumar Funtuwa,wanda makarantun Islamiyoyi da na Tsangaya sama da 430 suka halarta a ranar Asabar da ta gabata a karamar Hukumar Funtuwa ta jihar Katsina.

A Jawabinsa, Khalifa Aliyu Sa'idu Alti ya kara da cewa, kar mu bari makiya su shekar da jinanan mu don ran dan Adam ya fi daraja a wrurin Allah don haka na ke kira da babbar murya don Allah duk inda ke fama da matsalar tsaro su hakura da maulidin dare su yi shi  da rana, idan kuma da ranar akwai matsala sai a ciyar da abinci ga mabukata, in ji Kalifa Aliyu Sa'idu Alti. 

"Kuma ya yi kira ga jami'an tsaro da su taimaka wajen ba ma su yi Maulidi kariya da kuma shawara ta yadda ba ba za a samu salwanta rayuka ba.

A nasa jawabin shugaban kwamitin zagayen maulidin, Bashir Muhammad Kin (Busiri) ya bayyana cewa,sun samar da tsari na musamnan da yafi na bara da kuma isassun jami'an tsaro da 'yan Agaji a wannan zagayen dan ganin ba a samu matsala kamar bara ba kuma sama da makarantun Islamiyya da Tsangaya 430 suka halarci zagayen daga nan cikin jihar Katsina da Kaduna da Zamfara.

A nasa jawabin gwamnan Jihar Katsina, Dr Diko Umar Radda da ya samu wakilicin, babban memba a Hukumar Hizbah ta jihar Katsina, Kamal Sheikh Alti ya bayyana cewa, mai girma gwamna Radda yana tare da mu wannan zagayen kuma ya ce na shaida muku cewa, gwamnatin Jihar Katsina, ta ware tallafin gudummawa na zagayen gari na kowacce karamar Hukumar da ke fadin jihar Katsina, za a tura ma kowanne kwamitin zagayen na su tallafin.

A kan haka ne muke kira da a ci gaba addu'a don ganin kudirin gwamna Radda ya cika na samun nasara tsaro da aiwatar da ayyukan ci gaban al'ummar jihar Katsina baki daya.


No comments