Jagoran Harkar musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya jajantawa al'ummar jihar Borno musamman mutanen birnin Maiduguri bisa i...
Jagoran Harkar musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya jajantawa al'ummar jihar Borno musamman mutanen birnin Maiduguri bisa ibtila'in ambaliyar ruwa da ya auku.
Shaikh Zakzaky ya bayyana hakan ne a ranar Laraba 11 ga watan Satumban 2024 a cikin wata sanarwa da ofishin Shehin malamin ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Facebook, inda ya yi kira ga hukumomi da su ɗauki duk matakan da suka dace domin gyara ɓarnar da aka samu.
Ya kuma yi addu'ar Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu, ya kuma gaggauta kawo samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata.
Sanarwar ta soma da cewa; "Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Ƙai. Sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ke aukuwa a jihar Borno, wanda ya yi sanadiyar rashin rayuka da jikkata jama'a masu yawa, tare da hasarar dukiyoyi da dama, Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky na jajanta ma iyalan dukkan waɗanda wannan bala'i ya shafa. Ya yi kira ga hukumomi da su ɗauki duk matakan da suka dace domin gyara ɓarnar da aka samu.
"Jagora ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya jiƙan waɗanda suka rasu, Ya kuma gaggauta samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata", sanarwar ta ƙarƙare.
No comments