Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Rikicin Barkuta: Bai da nasaba da kabilanci ko tsakanin Fulani da Gwarawa - Hon. Rabe

Daga Awwal Umar Kontagora An bayyana rikicin da yayi sanadiyar lakume rayuka da dukiyoyin jama'a a yankin Barkuta na gundumar Beji a kar...



Daga Awwal Umar Kontagora

An bayyana rikicin da yayi sanadiyar lakume rayuka da dukiyoyin jama'a a yankin Barkuta na gundumar Beji a karamar hukumar Bosso da ya auku a kwanakin baya bai da nasaba da kabilanci ko Fulani makiyaya da Gwarawa manoma. Domin tsakanin su ba gaba kuma babu wani sabani a tsakanin su.

Kwamishinan ma'aikatar kula da jin dadin manoma da makiyaya, Hon. Umar Ahmad Sanda ( Rabe) ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Minna.

Kwamishinan yace rikici ne na daukar doka a hannu wanda ya faru tsakanin yan sa kai, wadanda ma wata kila hukuma ba ta san da zaman su ba, suka aikata wannan mummunar aikin, amma duk wanda yace rikici ne tsakanin Fulani da Gwarawa ne to ba gaskiya ba, domin dukkanin bangarorin nan biyu suna da kyakkyawar fahimtar juna.

Hon. Rabe, cikin ikon Allah bisa wasu matakan da gwamnatin jiha bisa jagorancin mataimakin gwamna, da fadar mai martaba sarkin minna, an kafa kwamiti kuma sun ziyarci yankin dan sanin hakikanin abinda ya faru, wanda da yardar Allah za a dauki kwakkwarar mataki akan wannan lamarin dan gudun faruwar hakan a gaba.

A hukumance za mu bi salsalar faruwar lamarin kuma gwamnati za ta tabbatar hakan bai sake faruwa a gaba in Allah ya yarda.

Dan haka muna godiya ga Allah, kuma godiya ga masu ruwa da tsaki da suka tsawatar kuma an samu sauki sosai, domin bayan ziyarar gwamna mai riko Comr. Yakubu Garba ya ziyarci yankin ya bincika kuma ya dauki matakan da suka dace, haka mai martaba sarkin Minna, Dr. Umar Faruq Bahago na yada kwamiti bayan su yi ta'aziyya kuma sun tabbatar da yin kwakkwarar bincike wanda ina da tabbacin masarauta za ta dauki tsauraran matakan da suka dace dan ganin hakan bai sake faruwa a gaba ba.
Kwamishinan, ya shawarci al'umma cewar akwai sarakunan gargajiya, akwai rundunan yan sanda, akwai jami'an tsaron farin kaya ( DSS), duk lokacin da mutum ya ga abinda bai gamsar da shi ba, ya sanar iyaye sarakunan gargajiya ko jami'an tsaro mafi kusa da shi. Ba daidai ba ne idan abu ya faru na rashin fahimta mutum ya dauki doka a hannun sa ba, mu shugabanni wajibin mu ne ko a wace kabila ko addini mutum ya ke yi idan aka zalunce shi mu bi masa hakkinsa, duk abinda zai kawo zaman lafiyar al'ummar kasar mu dole ne mu tabbatar da shi.

Saboda ina kara janyo hankalin jama'a da su yi hakuri a zauna lafiya, domin fitina fa idan ta tashi ba a san inda za ta tsaya ba, kuma bai kawo cigaba balle kuma a samu karuwar arziki, inji shi.

No comments