Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Hajiya Maryam Abacha ta yi ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar ‘Yar’adua

Matar tsohon shugaban Nijeriya, Marigayi Sani Abacha, wato Hajiya Dakta Maryam Abacha ta mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan Alhaji Musa ‘Yar’...


Matar tsohon shugaban Nijeriya, Marigayi Sani Abacha, wato Hajiya Dakta Maryam Abacha ta mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan Alhaji Musa ‘Yar’adua bisa rasuwar mahaifiyar tsohon shugaban Nijeriya Marigayi Umaru Musa Yar’adua. 

Hajiya Maryam ta mika sakon ta’aziyyar na ta ne a yayin zantawa da ‘yan jarida a birnin Tarayya Abuja. Hajiya ta ce tabbas an yi rashin mahaifiyar Umaru Musa, domin mace ce mai albarka. Inda ta yi addu’ar Allah ya jikan marigayiyar ya kuma santa a ajannah. 

Hajiya Maryam ta soma da cewa; “innalillahi wa’inna ilaihi raji’un. Iyakacin karfinmu ke nan na dan Adam. Karshen dan Adam ke nan mutuwa. 

“ina mika ta’aziyyata a madadina da iyalina zuwa ga iyalin marigayi Alhaji Musa Yar’adu’a da iyalan marigayi Janaral Shehu Yar’adua da iyalan marigayi Umaru Yar’adua; Allah ya jikanta ya yi mata rahama. Allah ya samu a damshinta”, ta yi addu’a. 

Ta ci gaba da cewa, “mace ce mai albarka, ta haifi shugaban kasa, ta haifi mataimakin shugaban kasa, ta haifi yara, ta yi shekaru. Allah yasa mu ma mu zama irinta. Allah yasa kowa ya zama irinta. Allah ya jikanta ya yi mata Rahama. Allah ya sa aljannah makoma, kuma Allah ya ba mu hakurin rabuwa da ita. 

Hajiya Binta Dada Musa ‘Yar’adua, mahaifiyar tsohon Shugaban Nijeriya, marigayi Umaru Musa ‘Yar’adua, ta rasu ne a ranar Litinin 2 ga watan Satumban 2024 da karfe 8 na dare, a Asibitin Koyarwa na Katsina. Ta rasu ta na da shekaru 101 a duniya. 


No comments