Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

NUMW Ta Jaddada Goyon Bayan Ta Kan Kafa ‘Taskforce’ Da Gwamnatin Neja Ta Yi

Daga Awwal Umar Kontagora Kungiyar leburori masu hakar ma'adanin kasa, reshen jihar Neja ta jaddada goyon bayan ta kan kafa Tasksforce d...


Daga Awwal Umar Kontagora

Kungiyar leburori masu hakar ma'adanin kasa, reshen jihar Neja ta jaddada goyon bayan ta kan kafa Tasksforce da gwamnayin Neja tayi.

Shugaban kungiyar a jihar Neja, Kwamared Musa Adamu Nasko ya yi yabon lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna.

Nasko, ya ci gaba da cewar yanzu haka gwamnatin ta damka alhakin tara kudaden shiga a hannun wasu kamfanoni biyu, MARUFAWA Of Concept and Project Limited, da zai kula da kananan hukumomin Chanchaga, Shiroro, Munya da Bosso, Suleja. Sai kamfanin KIFFMA da zai kula da Magama, Mashegu da Rijau, dan haka ina kira ga 'ya'yan kungiyar mu da su bai wa wadannan kamfanonin hadin kai, musammam 'yan kasuwar Minna domin gwamnatin jihar mu ta dora masu wannan aikin, kuma mun fahimci aikinsu aikin cigaban jiha ne baki daya. Muna kokarin hada su da dukkanin yayan kungiyar mu na wadannan kananan hukumomin, domin aikin yazo masu cikin sauki. Kamar yadda muka sha fadi ne a kowani lokaci kofar mu a bude take duk wata hanyar da za ta kawo cigaba kuma zai taimaka wajen bunkasa hanyoyin samun kudaden shiga ga gwamnati indai za a sakar mana mara wajen bin ka'ida a shirye muke dan mu taimakawa gwamnati wajen isar da manufofinta cikin sauki ba tare da turjiya ba.
Akwai kamfanonin hakar ma'adanai sama da dari biyar a jihar nan, amma wadanda suka gabatar da kan su ga hukumomin jiha ba su wuce dari biyu ba.

To ke nan, duk wani kamfanin da aka baiwa aikin nan, zai shigo ne a matsayin makaho, domin bai san aikin ba, bai san inda ma'aikatan suke ba, muna ne muke fagen kuma mu ne za mu yi ma shi jagora mu kai shi duk inda ya kamata, muna yin hakan ne saboda alakar mu da gwamnatin jiha, mun yi kiraye kiraye da dama, kuma daga karshe Allah ya amsa, gwamnati ta saurari kiraye kirayen mu ka ga wannan cigaba ne sosai.

Ba abin da ya kamata mu yi wa gwamnatin, sai godiya kuma mu bata hadin kai wajen cin ma wannan kudurin na ta.

Aikin wadannan kamfanonin ne a matsayin 'consultant' zai bai wa gwamnatin jiha samun hakikanin inda matsalolin suke, yanzu gwamnatin jiha ta cire dakatarwar da tayi na wucin gadi, bisa wasu ka'idodi wanda muna da tabbatacin idan ta sakarwa kwamitin State Tasksforce abubuwan da suke bukata, zai taimaka gaya wajen sanya idanu yadda ya kamata da samarwa gwamnati kudaden shiga.
Saboda duk wani kamfanin ma'adani da ya cika ka'idarsa zai cigaba da aiki ba tare da wata tsangwama ba, haka kuma duk leburan da yabi ka'idodin kungiya wanda gwamnati ta amince da shi zai cigaba aikinsa ba tare da fargaba ko tsoron kamu ba.

Mai girma mataimakin gwamna, a ranar da ya rantsar da wannan kwamitin na Taskforce yace akwai kamfanoni sama da dari biyar da suke da rajista amma sama da dari biyu suka gabatar da kan su ga gwamnatin jiha, gaskiya muna nan a kungiyance muna wayar da kan masu kamfanonin da su tabbatar sun bi ka'idodin gwamnatin jiha saboda dalilan tsaro wanda hakan zai ba su kwarin guiwar cigaba da aikinsu ba tare da tsangwama ba.

No comments