Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

DSS Ta Kashe Ƴan Bindiga Ta Ƙwato Buhunan Makamai A Neja

Daga Awwal Umar Kontagora An kama buhuna cike da abubuwa da ake kyautata zaton bindigogi ne da kuma tsabar kudi a hannun wasu da...


Daga Awwal Umar Kontagora

An kama buhuna cike da abubuwa da ake kyautata zaton bindigogi ne da kuma tsabar kudi a hannun wasu da ake tuhumar yan bindiga ne yayin wani samamen jami'an tsaron leken asirin farin kaya.

Hukumar tsaro ta DSS ta hallaka ’yan bindigar biyu tare da kama wasu da dama a kauyen Hayin-Nasara da ke yankin Tafa a jihar Neja.

’Yan bindigar sun gamu da ajalinsu ne a hannun jami’an DSS  a yankin da ke kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Hukumar DSS ta ragargaji ’yan bibdigar ne a wani samame na musamman da ta kai a wasu rugagen Fulani da ke wajen garin Tafa a ranar Juma’a.

Wata majiya a DSS ta shaida ma wakilinmu cewar a yayin samamen an kama wasu buhuna cike da wasu abubuwa da ake kyautata zaton bindigogi ne da tsabar kudi, a cikin wani bukka.

Wani mazaunin kauyen Hayin-Nasara ya shaida mana cewa, “mun je mun ga gawar wadanda ake zargin, shi kuma dayan, wanda ake wa lakabi da ‘pointer’, jami’an tsaron sun tafi da shi.’’

Wani dan banga a yankin ya ce,  “Daga bayana sojoji sun zo daga Abuja suka kokkona bukkoki da dama a rugar.”

A cewarsa, wasu daga cikin wadanda ake zargin sun dade da zama a yankin.

Amma ya ce akwai wadanda suka dawo kwanan nan domin sun buya sakamakon ragargazar da suke sha daga jami’an tsaro a daji.

Zuwa. hada rahoton dai, ba wani kwakkwarar bayani daga rundunar yan sanda ta jihar Neja kan faruwar lamarin.

No comments