Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Kebbi ta kafa Kwamitin musamman kan matsalar ambaliyar ruwa

Daga Awwal Umar Kontagora Majalisar gudanarwar Jihar Kebbi ta amince da kafa wani kwamiti na mutane 16 da za su yi aiki akan hanyoyin da za...


Daga Awwal Umar Kontagora

Majalisar gudanarwar Jihar Kebbi ta amince da kafa wani kwamiti na mutane 16 da za su yi aiki akan hanyoyin da za'a magance  matsalar afkuwar ambaliyar ruwa  a jihar.

Kwamitin zartarwar ta amince da hakan ne a wani zaman da ya gudana ranar laraba da ta gabata a karkashin jagorancin Gwamna Kwamared Dakta  Nasir Idris Kauran Gwandu.

Haka kuma sanarwar ta fito ne ta bakin kwamishinan yada labarai da raya al'adu, Alhaji Yakubu Ahmed Birnin Kebbi, yayin da yake wata ganawa da yan jarida jim kadan bayan kammala taron.

Kwamishinan ya kara da cewar gwamnati ta amince da nadin kwamitin ne nan take domin samar da hanyoyin magance matsalolin ambaliyar ruwa da ake fuskanta a wasu kananan hukumomin jihar.

Ya kara da cewar hasashen yanayi ya nuna za'a samu matsalar ambaliyar ruwa a jihar, sannan yace koda yake hasashe ne ba lallai ya zama gaskiya, amma gwamnatin Kebbi ba zata jira sai ya auku ba, dole zata yi kokari gwargwadon hali wajen dakile wannan matsalar domin kuwa mun ga yadda ambaliyar ruwa a bana ya yiwa wasu jihohi a kasar nan.

Kwamishinan ya cigaba cewar hukumar bada agajin gaggawa ta NEMA ita ma ta bayar da sanarwar samun ambaliyar ruwa wanda zai iya afkuwa daga wajen Nijeriya wanda zai iya shafar wasu sassan jihar Kebbi wanda hakan na daga cikin dalilan da suka sanya gwamnati kafa wannan kwamitin karkashin jagorancin mataimakin gwamna Sanata Umar Abubakar Tafida domin samar da hanyoyin magance wannan matsalar.

Ya kara da cewar suna sane da gargadin da hukumomi suka yi na yi yuwar samun ambaliyar ruwa daga Central Guinea, Futa Jalo Highland region, River Senegal, River Gambia da kuma River Niger wanda aka ce ambaliyar ruwan su zai iya shafar wasu yankuna na kasar nan.

Kwamishinan ya bayyana cewar daga cikin rahoton hasashen da suka samu ya nuna cewar ambaliyar ruwan za ta shafi Jihar Kebbi inda za tafi shafar karamar hukumar mulkin  Bunza ta jihar Kebbi.

Kwamitin zai fara aikin sa ranar Alhamis inda zai hadu da shugabannin kananan hukumomin Jihar yayi musu bayani su kuma su yiwa sarakunan gargajiyar yankunan su bayani akan matsalar.

Daga cikin aikin kwamitin shi ne gano wuraren da ambaliyar ruwan zai iya shafa kai tsaye a jihar domin hada kai da malaman addini da sarakuna domin sanar da al'umma har ma idan ta kama a kwashe al'umma daga yankunan.

Gwamnatin Jihar Kebbi za ta tabbatar tayi dukkanin abinda ya dace wajen ganin ba'a samu matsala ba da yardar Allah inji Kwamishinan.

Daga cikin sauran mambobin kwamitin sun hada da:

1. Kwamishinan yada labarai da raya al'adun jihar Kebbi 
2. Kwamishinan harkokin jinkai wato Humanitarian Affairs 
3. Kwamishinan harkokin ruwa.
4. Kwamishinan ilimi mai zurfi 
5. Kwamishinan harkokin addinai 
6. Kwamishinan ayyuka na musamman wato Special Duties 
7. Kwamishinan harkokin muhalli wato Environment 
8. Kwamishinan kiwon lafiya 
9. Kwamishinan kudi 
10. Kwamishiniyar harkokin mata 
11. Kwamishinan harkokin tsare-tsaren kasa da raya birane 
12. Kwamishinan matasa da wasanni 
13. Kwamishinan ayyuka 
14. Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kebbi wato SEMA da dai sauransu.



No comments