Wata mahaifiya da ambaliyar Maiduguri ta ritsa da ita, ta ce suna matuƙar buƙatar abinci a sansanin Bakassi da aka ajiye su. Falmata Goni ...
Wata mahaifiya da ambaliyar Maiduguri ta ritsa da ita, ta ce suna matuƙar buƙatar abinci a sansanin Bakassi da aka ajiye su.
Falmata Goni ta ce ta kuɓuta daga gidansu wanda ruwa ya cinye tare da ƴaƴanta bakwai, kafin hukumomi su kwaso su a mota.
Mahaifiyar wadda ga alama tana cikin halin kaÉ—uwa ta ce ba ta iya samun abinci sai dai kawai ta sha ruwa kuma a hakan ta shayar da jaririnta.
A cewarta, sauran ƴaƴan nata na samun abin da suke ci ne daga ɗan tallafin da suka samu a maƙwabta.
Hukumomi a jihar Borno sun ce mutane kimanin miliyan biyu ne ambaliyar ruwan ta shafa a birnin Maiduguri.
No comments