Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tallafin Bosso Karami Ya Zama Santurakin Cikasoron Minna

Daga Awwal Umar Kontagora Tallafin Bosso Karami, Amb. Dakta Nura Hashim ya zama Santurakin Cikasoron Minna, Alhaji Sulaiman Yahaya Babangida...



Daga Awwal Umar Kontagora

Tallafin Bosso Karami, Amb. Dakta Nura Hashim ya zama Santurakin Cikasoron Minna, Alhaji Sulaiman Yahaya Babangida. Nadin na sa ya biyo bayan jajircewarsa wajen tallafawa matasa da karfafa guiwarsu wajen dogaro da kai, musamman ta fuskar nusar da su muhimmancin Sana'a, siyasa da rungumar harkar noma ka'in da na'in.

Amb. Nura Hashim, wanda shi ne mataimakin shugaban kungiyar manoma ta jihar Neja kuma sakataren kungiyar manoma auduga, sannan shugaban kungiyar manoman alkama, kuma mataimakin shugaban kungiyar manoman tumatur a jihar Neja.

Nadin ya biyo bayan wata ziyarar shugaban kungiyar hadin kan Hausa da Hausawan duniya Charitable Foundation, Alhaji Muhammad Saeed Ghana da ya kawo jihar inda aka nada Amb. Nura a matsayin kodinetan jihar Neja.

A yayin ziyarar babban sakataren kungiyar na duniya kuma shugaban kungiyar a Nijeriya,, ya ziyarci tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida da wasu manya a jihar dan karfafa guiwar hadin kan Hausawan jihar da sauran Hausawan duniya wajen dawo da zumunci, taimakekeniya da bunkasa harshen Hausa.

Babban sakataren kungiyar Hadin Kan Hausa Da Hausawan Duniya Charitable Foundation, Alhaji Muhammadu Saeed Ghana, a bayaninsa yace ya kawo ziyarar ban girma da jinjina ga al'ummar jihar Neja, domin samar da hadin kai, zaman lafiya, da cigaba a tsakanin dukkanin kabilu. A yayin ziyarar tasa, ya gana da manyan sarakuna da masu ruwa da tsaki, inda ya jaddada muhimmancin zaman lafiya da hadin kai al'umma.

Alhaji Muhammadu Saeed Ghana, ya bukaci hadin kai da zaman lafiya a tsakanin dukkanin kabilu, da samar da fahimtar juna da kuma cigaban kasa da hadin guiwar wajen lalubo matsalolin da al'umma ke ciki dan walwale su.

Alhaji Saeed Ghana ya bayyana  Alhaji Suleiman Yahaya Babangida ( Cikasoron Minna ) a matsayin mataimakin shugaban kungiyar ta kasa, tare da jinjina kwazonsa da jagorancin da yake baiwa al'umma da taimakon mabukata da hadin kai.

Cikasoron Minna kuma mataimakin shugaban kungiyar ta kasa ya tabbatar da nadin Amb. Dr. Nura Hashimu (Tallafin Bosso karami ) a matsayin sabon shugaban kungiyar na jihar Neja.

Kungiyar Hadin Kan Hausa Da Hausawan Duniya Charitable Foundation na nufin tallafawa da karfafa guiwar al'ummar Hausawa a duniya wajen dogaro da kai da zaman lafiya tsakaninsu da sauran kabilu. Kungiyar wadda ke da hedikwatarta a jihar Kadunan Nijeriya, ta mayar da hankalin ta ne kan harkokin ilimi, kiwon lafiya, da inganta tattalin arziki da taimakawa al'umma don samun dogaro da kai wajen samun rayuwa mai inganci.

Da yake jawabi bayan nadin nasa, Amb. Dr. Nura Hashim ya sha alwashin cigaba da jajircewa wajen ganin ya sauke nauyin da aka dora masa, haka kuma ya bayyana cewar al'umma Hausawa, al'umma ce da aka sani da son zaman lafiya, da jajircewa wajen dogaro da kai.

Saboda haka, zan shiga lungu da sako wajen wayar da kan al'umma muhimmancin zaman lafiya, wayar da kai wajen dogaro da sana'a da rungumar harkar noma ka'in da na'in musamman ga matasa da ake sa ran sune shugabannin gobe.

Ambasadan, ya kara jawo hankalin gwamnati akan matsalar tsaro da ya addabi kasar nan, wanda hakan ya mayar da tattalin arzikin kasar baya sosai. Akwai bukatar al'ummar kasar nan su kawar da bambance bambancen da ke tsakanin su, na harshe ko addini, su hada kai dan gina sabuwar Nijeriya.

Nura Hashim, ya nemi yan siyasa da masu hannu da shuni da su tabbatar sun bada gudunmawa kan kudurin gwamnati na cigaban kasa, zaman lafiya, dan cigaban tattalin arzikin kasar nan.

Dokta Nura Hashim, wanda ke rike da lambar yabo na jakadancin zaman lafiya ( Peace Ambassador) na Leeway Peace and Human Right Foundation, ya samu lambar yabo da dama daga kungiyoyin zaman lafiya na duniya, masu zaman kan su, kan jinkai da tausayin al'umma. Haka kuma ya samu sarautu da dama daga gundumomi da dama a jihar, wanda ya hada da Tallafin Bosso Karami, Talban Tatiko, kuma Jarumin Tutungo sannan kuma Santurakin Cikasoron Minna. 

No comments