KIRA GA GWAMNATIN JIHAR KADUNA DA TA DAINA AMFANI DA KARFIN MULKI TA HANYAR CI GABA DA TSANANTAWA DA TAKURAWA 'YAN SHI'A A JIHAR. ...
KIRA GA GWAMNATIN JIHAR KADUNA DA TA DAINA AMFANI DA KARFIN MULKI TA HANYAR CI GABA DA TSANANTAWA DA TAKURAWA 'YAN SHI'A A JIHAR.
Tun bayan kisan kiyashin da aka yi a Zariya a shekarar 2015, a bayyane yake cewa gwamnatin jihar Kaduna ta siyasantar da rayuka da dukiyoyin al’ummar Shi’a a jihar ta hanyar kashe-kashe, barazana, tsoratarwa da ruguza kadarori.
A ranar Lahadi 21 ga watan Oktoba, 2024, mun samu labarin cewa bayan sanarwar da aka fitar da misalin karfe 6:000 na yammacin ranar Juma’a, 19 ga watan Oktoba, 2024, gwamnati ta aika da wata babbar mota kirar buldoza da tsakar dare tare da rakiyar jami’an tsaro rirrike da bindigogi, sun ruguza gidan Injiniya Yahya Gilima da ke No. 11 Yahaya Imam Road Malali GRA, Kaduna.
A matsayinsa na musulmi na gari, Injiniya Gilima dai ya bi doka da oda da kuma cika sharuddan izinin zama da mallakar wuri kamar yadda gwamnatin jihar Kaduna ta gindaya, kuma ya shafe sama da shekaru 22 yana zaune lafiya a gidansa.
Muna Allah wadai da wannan zalunci da nuna son zuciya da dabbanci a kan dan kasa wanda bai aikata wani laifi ba
’Yan Najeriya su sani cewa Gwamnatin Jihar Kaduna da ta shude ta Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i da gwamnatin mai ci a karkashin Sanata Uba Sani duk suna da laifin take hakkin ‘yan Shi’a na jihar.
A daidai wannan lokaci yana da kyau a ce mai girma Gwamna Uba Sani ya gane cewa ‘yan Shi’a suna ko’ina a duniya, ciki har da Saudiyya da sauran wurare a yankin Gabas ta Tsakiya, don haka duk wani yunkuri na kawar da mabiya Shi’a a jihar Kaduna zai haifar da fargaba da firgici ne na dindindin a jihar, musamman ma arewacin Najeriya baki daya.
Muna sa ran mai girma Gwamna ya mai da hankali ne kan manufofi da ayyukan da za su tabbatar da zaman lafiya tare da ciyar da ci gaban zamantakewa da tattalin arziki a jiharsa. Muna ba da shawarar cewa ya kamata Gwamna ya nemo sahihiyar hanyar tabbatar da bayanan tsaro da jami’an tsaro ke bayarwa, wadanda a mafi yawan lokuta, suna yin amfani da bayanan sirri kirkirarru don samun kudi daga aljihun gwamnati don amfanin kansu.
Muna ba da shawarar cewa mai girma Gwamna ya yi taka-tsantsan don kada ya haifar da tarzoma a cikin al'umma don neman biyan bukatar wani mutum guda. Muna kuma ba mai girma shawarar da ya mayar da hankali wajen yi wa al’ummar jihar Kaduna hidima, maimakon kula da muradun masu rike da madafun iko da iyayengidansu na kasashen waje.
Daga karshe muna rokon Allah ya kare Najeriya da Arewacin Najeriya musamman.
Mun gode.
SA HANNUN:
Jami’in hulda da jama’a na kasa
Abdullahi Hassan Shazy
Wannan kungiya ta All Ja'afariyya Shia Muslim Community in Nigeria ta yi rajista tare da Hukumar Harkokin Kasuwanci (CAC) tun daga 1999. Kuma tana wakiltar buri da muradun ‘yan Shi’ar Nijeriya ne.
No comments