Daga Awwal Umar Kontagora Hukumar da ke wayar da kai kan muhimmancin ilimin yaya ma ta shirya taron wayar da kan tallafin kara...
Daga Awwal Umar Kontagora
Hukumar da ke wayar da kai kan muhimmancin ilimin yaya ma ta shirya taron wayar da kan tallafin karatu ga yaya mata a jihar Neja. Tunda farko a bayanin ta Kodinetan shirin, Hajiya Maimuna Ibrahim Tahir, ta bayyana cewar hukumar ta shirya taron ne ga sarakuna, da shugabannin addinai da shugabannin al'umma kan shirin bada tallafin karatu ga yaya mata dan karfafa guiwar iyaye wajen rage yawaitar cire yaya mata da zaran sun kammala karatun faramare, wanda tsoron talauci ko ganin rashin muhimmancin ilimin boko ga yaya mata.
Bincike dai ya nuna kashi hamsin cikin dari na yaya mata basa zuwa makarantar gaba da famare, yayin da kusan yaya mata miliyan daya ke barin makaranta a shekarar farko ko shekarar karshe na kammala karatun faramare. Wanda ya shafi mata yan shekaru goma zuwa sha tara da haihuwa, bisa kididduga su ke da kashi ashirin da uku na al'ummar kasar nan.
Hukumar AGILE, wadda ta mayar da hankali kan bada tallafin karatu da koyar da sana'o'in hannu ga mata, tace akwai bukatar takaita auren wuri, dan kaucewa tilasta kananan yara haihuwa da wuri tun ba su yi kwari ba, dan inganta lafiyarsu, da samar sana'o'i domin samun damar dogaro da kan su dan bunkasa tattalin arzikin al'umma da samun rayuwa mai inganci.
Hajiya Maimuna, tace akwai bukatar mu dauki dukkanin matakan da suka dace dan samar da ingantaccen ilimi da samar da rayuwa mai inganci ga yaya mata.
Shirin bada tallafin dai zai fara da kananan hukumomi goma sha biyar cikin ashirin da biyar na jihar Neja a matakin farko.
Tace manufar shirya taron shi ne yadda za a binciko yara mata dan ba su tallafin kudi dan karfafa guiwar iyaye wajen bada kulawa ga ilimin yayan su mata kyauta.
Shirin dai an bullo da tsare tsare wanda dole sai yarinya ta samu kashi saba'in na abinda ake bukata.
Da yake bayani a taron, hakimin Bosso, Alhaji Mu'azu Adamu Laka, ya yabawa ma'aikatar ilimin sakandare na jihar Neja, da hukumar AGILE wajen wannan yunkurin dan dakile matsalolin rashin baiwa ilimin yaya mata muhimmanci ganin irin damar da suke baiwa al'umma wajen samun rayuwa mai inganci.
Alhaji Laka, yace baiwa mace daya ilimi tamkar baiwa al'umma masu yawa damar samun rayuwa mai inganci ne saboda tausayi da irin kulawar da suke baiwa cigaban yara masu tasowa.
Babbar daraktan bada tallafin ilimin yara, Hajiya Maryam Audi Abdurahim, kuwa tace wajibi ne al'umma ta tashi tsaye wajen ganin an bada gudunmawa dan ilmantar da yaya mata, musamman ganin yadda rayuwa ta canja muddin baka da ilimi ko mai muhimmancin ka, ba wani gurbin da za ka taka na taimakawa iyalai.
Maryam Audi, tallafin kyauta ne amma dole sai an bi ka'idodin da muka tsara, ta yadda yarinya za ta samu kashi saba'in na halartar karatu.
Muna da jami'an da muka horar ta yadda zasu samo mana abinda muke bukata, kuma zasu yi aiki da rajistan da ke dauke da sunayen yaran ne na makarantun da suke.
Augi, ta cigaba da cewar za a dauki cikakken bayanai masu kulawa da yaran ne, ta yiwu uwa ce ko uba kuma za a bada kudaden ne kai tsaye, dan karfafa guiwar masu kulawa da yaran. Ta yadda in ma talauci ko wani ke assasa cire yaran mata daga makaranta zasu damar anfani da kudin wurin kawar da shi.
Yanzu hakan jahohi goma sha bakwai na kasar nan ne zasu ci moriyar shirin, inda muke sa ran baiwa yara mata a kallan miliyan daya ba su wannan tallafin.
A jihar Neja, muna da kudurin ganin a kallan yara mata a kallan dubu talatin zuwa hamsin sun ci moriyar wannan tallafin.
Taron dai ya samu halartar masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi ta jihar Neja, inda kwamishinan ma'akatar kula ilimin bai daya na makaranttun sakandaren jihar Neja ta samu wakilcin Hajiya Hadiza Zukogi.
An gabatar da ƙasidu da dama masu ƙarfafa guiwa da hanyoyin da za a bi wajen cin gajiyar wannan shirin.
No comments