Daga Idris Umar, Zariya A cikin makon da ya gabata ne wasu ƴan sanda masu gadin gidan man Danco wato (Danco fillin station) dake...
Daga Idris Umar, Zariya
A cikin makon da ya gabata ne wasu ƴan sanda masu gadin gidan man Danco wato (Danco fillin station) dake Abeokuta a hanyar zuwa Legas sun yi ƙoƙarin kashe wani matashin direba mai suna Ɗahiru Ahmad mai shekaru 35 ma'aikacin kamfanin Bilga transport dake Fatakwal.
Wakilinmu ya saurari matashin direba a yayin da yake zantawa da manema labarai game da lamarin.
Malam Ɗahiru ya shaidawa manema labarai cewa bisa yadda suke bin hanyar ta Legas da dare da rana wani lokacin sukan tsaya a gidan mai domin shan mai ko hutawa ko gyara.
Ɗahiru ya ce, a wannan ranar da lamarin faru ya tsaya ne a gidan man (Danco filing Station) na hanyar zuwa Legas don shan mai domin nan ake tura su shan mai. Ya ce anan ne ya tarar da ƴan sandan da suke gadin gidan Man suna yin hayaniya da wasu matasa amma sun kora su sun bar gidan man sun tafi gaba.
Malam Ɗahiru ya ce, wasu dake wurin suka ba shi shawara da ya janye motarsa a wajen sai ya ce to babu damuwa bari ya koma gaba.
Malam Ɗahiru ya ci gaba da cewa; ya je gaban motarsa ke nan har ya buɗe don ɗauke ta daga gefen gidan man sai wani Ɗan sanda mai aiki a gidan man ya zo ya buga mishi Itace a kafaɗarsa ba tare da yin wata tambaya ba.
Ɗahiru ya ce, kafin ka ce me sauran abokan aiki Ɗan sandan suma suka ƙaraso wajen suka yi ta buga mishi kan bindiga a kanshi har sai da suka ga ba ya ko motsawa, in ji shi.
Bayan da suka ga kamar ya mutu ne sai suka gudu suka bar shi a wannan waje cikin jini warwas.
Ganin halin da Ɗahiru ya shiga ne sai wasu Hausawan dake wajen suka hango abin da ke faruwa sai suka ƙaraso wajensa suka ɗauke shi cikin jini suka kai shi gidan Sarkin Hausawan wannan Unguwa na gidan man (Danco filling station) domin ɗaukar matakin da ya dace tare da ceto ransa.
Sarkin Hausawan ya yi ƙokarin sosai har ma ya kiran ofishin da Malam Ɗahiru yake aiki da su domin sanar da su halin da direbansu Ɗahiru ke ciki don ɗaukar mataki.
Malam Dahiru ya tabbatar da cewa shi ba abin da ya haɗa su da ƴan sandan kuma bai yi laifin komilai ba illa kawai sun ganshi Bahaushe musulmi ɗan Arewa ne kawai.
"Abin tambaya a nan wanne laifi ɗan Arewa yake yi wa mutanen kudu? Shin me yasa rayuwar ɗan Arewa ta zama abin wulaƙantawa a Kudu?", ya tambaya.
Bisa hakan ne wakilinmu ya nemi jin ta bakin dangin wannan matashin direba akan wannan lamari. Malam Muhammad Abba, na ɗaya daga cikin dangin Malam Ɗahiru da aka raunata.
Malam Abba ya ce, suna kira ga hukumar ƴan sanda da su gaugauta ɗaukar matakin akan abin da ya faru da ɗan uwansu domin sun yi bincike babu laifin da ya yi musu illa ƙabilanci da wariyar harshe da bambancin addini da ya yi wa wasu ƴan kudu naso a zuciyarsu.
Abba ya ƙara da cewa bai kamata jami'in tsaro ya aikata abu ba tare da ya yi bincike na domin haka suke kira ga dukkan ƙungiyoyin direbobin Tirela da suke bin wannan hanya da su gaggauta yin bicike akan wannan lamari domin kaucewa matsalar da ka iya kawo saɓani a tsakanin al'umma.
Malam Abba ya ce ɗaukar mataki ya zama dole domin cin kashin da ake yi wa Hausawa ya yi yawa a kudu babu gaira babu dalili.
Ƙarshe ya godiya ga sauran aminan arziƙi da suka bayar da gudummawa ga Ɗan uwansa da shi kansa a yayin da lamarin ke faruwa kuma ya roƙi DPO na wannan yanki da ya yi bincike tare da yin adalci akan wannan lamari.
Bincike ya tabbatar da cewa yanzu haka Malam Ɗahiru na kwance yana jinya a garin su Zariya.
No comments