Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnan Jihar Kebbi Ya Amince Da Biyan ₦75,000 A Mafi Ƙarancin Albashi A Jihar

Daga Awwal Umar Kontagora Gwamnan jihar Kebbi, Kwamared Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu ya amince da biyan mafi karancin albashi...

Daga Awwal Umar Kontagora

Gwamnan jihar Kebbi, Kwamared Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu ya amince da biyan mafi karancin albashi na naira dubu saba'in da biyar ga ma'aikatan Jiha da kananan hukumomi.

Gwamnan kuma ya umarci kwamishinan kudi da babban akawun kudi na jihar da su tabbatar an fara biyan sabon mafi karancin albashin a cikin a wanni saba'in da biyu daga ranar Larabar makon nan.

Gwamnan ya amince da sabon mafi karancin albashin ne tare da sanya masa hannu a matsayin doka a gaban gamayyar kungiyar kwadago na jihar Kebbi.

Da yake jawabi a wurin taron sanya hannun akan kudurin dokar sabon albashin, gwamna yayi godiya ga kungiyar kwadago reshen jihar Kebbi bisa irin goyon bayan da suke bashi tun a lokacin yakin neman zabe har nasarar da ya samu a kotu.

Haka kuma ya bayyana cewar goyon bayan da suke ba shi ya kara masa kwarin guiwa wajen gudanar da aikinsa.

Shugaban kungiyar kwadago ta kasa, Joe Ajero da yake nasa jawabin a wurin taron, yayi jinjina ta musamman ga Gwamna Kwamared Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu bisa irin ayyukan cigaban al'umma da yake gudanarwa a fadin jihar duk da cewar jihar tana fuskantar karancin hanyoyin samun kudin shiga.

Ajero, ya zayyano irin ayyukan cigaban da  gwamnan ya gudanar a bangarori daban-daban da suka hada gyara da haskaka titunan babban Birnin jiha, ginawa da gyara makarantu da asibitoci, samar da takin zamani ga manoma kyauta, injinimin ban ruwa da kuma inganta jin dadi da walwalar ma'aikatan Jihar Kebbi baki daya.

Ajero, ya yabawa Gwamnan wajen biyan albashin ma'aikata akan kari, kudin gratuity,, fansho da kulawa da sauran bukatun ma'aikatan jihar.

A nasa hawabin, sakataren gwamnatin jiha, tun da farko, ya bayyana cewar kungiyar kwadago ta kawo tsarin sabon albashi na ₦72,000, ₦73,000, da kuma ₦75,000 inda Gwamna ya amince da nafi tsokan a cikin ukun na ₦75,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma'aikatan Jihar.

Shi kuwa, babban akawun kudi na jiha, Alhaji Bello Mahaliku da ya bayyana cewar gwamnatin jiha, za ta cigaba da biyan sabon mafi karancin albashin matukar Kwamared Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu ne gwamna, inda yayi kira ga ma'aikatan suma su kula da aikinsu sosai a matsayin godiya ga wannan kokari da gwamna yayi.

No comments