Daga Hassan Ibrahim Sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙaramar hukumar Zariya Injiniya Jameel Ahmad Muhammad yayi alƙawarin gudanar da...
Daga Hassan Ibrahim
Sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙaramar hukumar Zariya Injiniya Jameel Ahmad Muhammad yayi alƙawarin gudanar da aiyuka masu ma'ana wanda zasu inganta rayuwar al'umma acikin zamantakewa na rayuwa.
Injiniya Jameel ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan an ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasarar lashe zaɓen shugaban ƙaramar hukumar Zariya a ƙarƙashin jam'iyyar APC wanda hukumar zabe mai zaman kanta na jihar Kaduna ta bayar da sakamakon sanarwar.
Sabon shugaban na ƙaramar hukumar Zariya ya ce gwamnatin sa zata aiwatar da manufofi da dama wanda zasu kawo wa al'umma cigaba a fannoni da dama acikin zamantakewa na rayuwa,dan samar da shugaban ci na gari wanda al'umma zasu yi alfahari da shi.
"Akwai aikace aikace da dama da za muyi wa al'ummar ƙaramar hukumar Zariya wanda ya shafi ɓangaren ilimi,Kiwon Lafiya, Noma, koyar da mata Sana'o'i, gyaran muhalli da sauran su.Waɗannan kaɗan ne daga cikin abubuwan da za muyi dan ganin cewa alummar ƙaramar hukumar Zariya sun sami kyakkyawan shugabanci", a cewar sa.
Ya kuma bayyana cewa ƙofar sa a buɗe take wajen amsar shawarwari domin ciyar da al'ummar ƙaramar hukumar Zariya gaba.
Jameel Ahmad da jaddada yin aiki tare a matsayin tsintsiya maÉ—aurinkin ki É—aya dan samar da kyakkyawar shugabanci ta wannan fuska.
"Mu na sun goyon baya da haÉ—in kai da addu'o'i da kuma shawarwari yanda zasu samu nasarar gudanar da aiki."Ya ce.
Yayi godiya ga dukkan ƴan takara na jam'iyyu mabanbanta tare da kira a gare su da su zo a haɗa kai domin ciyar da al'ummar ƙaramar hukumar Zariya gaba, kasancewar su ma su na da rawar da zasu taka wajen bayar da shawarwari da kuma shigowa cikin gwamnati dan a haɗa ƙarfi da ƙarfe a yiwa jama'a abinda ya kamata.Inji shi.
Acewar Jameel Muhammad kasancewar ƙaramar hukumar Zariya akwai matasa da dama akwai tsare-tsare da zai samar wanda zai inganta rayuwar su na samun abinda zasu dogara dashi a rayuwa.
Ya na mai cewa akwai hanyoyi daban daban na koyar da matasa sana'o'i da kuma tallafa musu kan sana'o'i nasu.Fatan mu nan bada daɗewa ba a ƙaramar hukumar Zariya marasa aikin yi an rage su da yawan gaske su sami sana'o'i da zasu rike kansu dashi.
"Muna da tunanin gina kasuwanni kuma kowace kasuwa za muyi fannin sana'a daban. kasuwar ƴan waya ,Maɗinka,Kafintoci,,Maƙera, da sauran su.
Wannan za muyi ne dan mu ƙarfafa wa matasa su koyi waɗannan sana'o'in kuma ga dama ta samu, da kuma tallafa musu domin cigaba da gudanar da sana'ar ta su."Ya ce.
Kazalika sabon shugaban na ƙaramar hukumar Zariya yayi kira ga al'umma baki ɗaya na bashi goyon baya dan cimma manufofi da ƙudirori da yake dasu wanda zasu inganta rayuwar al'umma a fannoni da dama na rayuwa.
No comments