Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tallafin Marayu: Gwamnatin Kebbi Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Masu Almundahana Da Kudaden Marayu

Daga Awwal Umar Kontagora Gwamnatin  Kebbi ta dauki matakan gano bata gari da ke canza sunayen marayun da aka baiwa tallafi daga kungiyar ...

Daga Awwal Umar Kontagora

Gwamnatin  Kebbi ta dauki matakan gano bata gari da ke canza sunayen marayun da aka baiwa tallafi daga kungiyar 'World Muslim League' domin daukar dukkanin matakin doka da ya dace akan su.

Kungiyar World Muslim League dai ta bayar da tallafin kudi domin a baiwa marayu na ainihi a matsayin tallafin karatu da kuma abinci da sutura.

A wani binciken da  gwamnatin Kebbi ta gudanar, ta gano cewar akwai wasu ayyukan rashin gaskiya a cikin al'amarin.

Da yake zantawa da yan jarida, kwamishinan harkokin addinin musulunci, Hon. Muhammad Sani Aliyu ya bayyana cewar wannan al'amarin na canza sunayen ainihin marayu da dukkanin wani aikin rashin gaskiya a wannan al'amarin a matsayin cin amana da kuma zamba cikin aminci wanda gwamnati ba za ta lamunce shi ba.

Kwamishinan ya bayyana cewar daga cikin bayanan da suke samu, akwai wasu masu kula da marayu da suke hada kai da wasu bata garin jami'ai wajen cire kudaden da aka tura cikin asusun yara marayu da suke kula da su

Yace rahotanni da muke samu akan wannan tallafin, ya nuna cewar a wannan watan World Muslim League ta turawa yara marayu 1,849 kudi sama da biliyan biyu domin kula da karatunsu da al'amaran yau da kullum na rayuwarsu.

Kwamishinan ya kara da cewar yanzu haka gwamnati ta kafa kwamitin bincike domin gano inda aka karkata kudaden da aka cire ba bisa ka'ida ba daga asusun marayun domin dawo da kudin tare da hukunta dukkanin wanda aka samu da hannu a cikin lamarin.

Kwamishinan ya kara da cewar kwamitin ya kunshi kwamishinoni guda uku, masu baiwa gwamna shawara guda biyu, da kuma sakatarorin dindin din da kuma shi kan shi a matsayin shugaban kwamitin.

Kwamishinan ya bayyana cewar a binciken farko da suka gudanar sun gano cewar an gudanar da wannan aikin al'mundahanar ne ta hanyar amfani da POS a madadin ainihin bankuna kamar yadda aka saba.

Haka kuma ya bayyana cewar idan binciken su ya gano akwai hannun wani banki a ciki, to zasu rubuta takardar koke zuwa ga uwar bankin ta kasa domin daukar matakan da suka dace.

Kwamishinan ya bayyana wannan al'amarin da aka gudanar a matsayin zalunci ne bisa amanar marayu da aka basu inda ya bayar da da tabbacin gwamnatin jiha bisa jagorancin adilin gwamna Kwamared Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu ba za ta bar wannan abin ya tafi a banza ba, tabbas za'a kwatowa marayu hakkinsu kuma a hukunta masu hannu a ciki.

Kwamishinan yayi godiya ta musamman ga kungiyar ta World Muslim League da ta bayar da wannan tallafin inda kuma yace tuni sun sanar da kungiyar halin da ake ciki a ofishin ta da ke Kaduna inda suma su ka yi alkawarin bayar da dukkanin gudummawar da ta dace wajen magance faruwar haka a gaba. 

No comments