Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Muna Neman Tallafin Gwamna Umar Bago Kan Halin Da Muka Tsinci Kan Mu, In Ji Tsohon Kansila

Daga Awwal Umar Kontagora An nemi gwamna Umar Mohammed Bago da ya tallafawa al'ummomin da suka yi hasarar dukiyoyin su sakam...


Daga Awwal Umar Kontagora

An nemi gwamna Umar Mohammed Bago da ya tallafawa al'ummomin da suka yi hasarar dukiyoyin su sakamakon rikicin siyasar Kontagora kimanin shekaru ashirin da uku da suka gabata. Mun sani ba a lokacin shi aka yi wannan hargitsin ba, rikicin ya taso ne lokacin da zaben kananan hukumomi tsakanin PDP da PRP wanda ya auku lokacin mulkin marigayi Engr. Avdulkadir Kure.

Tsohon kansula, Hon. Dauda Mohammed ne yayi kiran, wanda yana daga cikin wadanda suka yi hasarar gidajen su sakamakon cin na wuta da matasan PRP suka yi na dukiyoyi da gidajen yayan PDP a lokacin.

Hon. Dauda, ya cigaba da cewar har ga Allah, marigayi Kure yayi yunkurin biyan diyya amma aka samu sabani tsakanin wasu manyan PDP da ake damawa da su, har gwamnatin ta shude a lokacin ba a ce mana komai ba.

Da yawa wasu mu, sun  rigamu gidan gaskiya sakamakon halin da suka samu kan su na bakin ciki da rashin taimakawa, mu kan mu ga mu nan rai kwakwai, mutu kwakwai. Yanda ka same ni a yanzu kai ma shaida ne muna cikin wani hali, kuma wallahi muna gwamnatin nan ta adali Umar Bago dari bisa dari, dan haka muna mika kokon bara ga adalin gwamna, da ya tallafa mana dan mu samu damar kulawa da iyalan mu kuma wallahi da yawan mu ba mu da kosasshen lafiya kuma ba abin jinya a tare da mu.

Ni kaina, bayan faruwan wannan lamarin sai da na shekara ban ga iyalai ba, saboda ban da yadda zan je kusa da su, da yawan mu yanzu mun zama yan gudun hijira mun bar mahaifar mu saboda hasarar da aka yi mana kuma yanzu haka a zaune muke ba abin yi.
Dangane da kimar barnar, idan za a binciki iyalan marigayi Barista Anache komai na hannunsa, domin a matsayin sa na lauya shi ya tattara komai, amma dai kan da yawan mu mun bar Kontagora, kuma nan da muke zama babu abin yi, muna neman alfarma ga adalin gwamnan mu da ya dubi Allah ya taimaka mana, mun sani ba bari a kwashe duka, amma ya taimaka mana za mu ji sanyi za mu samu kwarin guiwar komawa kusa da yan uwa da sauran iyalai dan cigaba da sauran rayuwar mu da su.
Ba mu iya komai ba, mafi yawan mu ba mu iya komai ba, in ban da siyasa amma yanzu idan mun samu tallafin gwamnati dole mu tsugunna mu samu madogarar rayuwa dan cigaba da rike iyalan mu.

No comments