Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

NNPP Ta Jihar Neja Ta Yabawa Gwamnatin Kano Kan Zaɓen Ƙananan Hukumomi

Daga Awwal Umar Kontagora Jam'iyyar NNPP a jihar Neja ta yabawa gwamnatin Kano kan yadda aka gudanar da zaben kananan hukumo...


Daga Awwal Umar Kontagora

Jam'iyyar NNPP a jihar Neja ta yabawa gwamnatin Kano kan yadda aka gudanar da zaben kananan hukumomi ba tare da tashin hankali ko fargaba ba. Shugaban jam'iyyar a jihar Neja, Hon. Awwal Muhammad Goma Kontagora ne yayi yabon ga manema labarai lokacin da yake tsokaci yadda zaben ya gudana.

Hon. Goma, ya cigaba da cewar a tarihin siyasar Kano da ma arewacin kasar nan ba a taba gudanar da zaben kananan hukumomi irin wannan ba, duk da tunka da warwara daga bangaren shari'a da rashin sanya hannun jami'an yan sanda kan zaben ban sanya gwamna Inijiya Abba Gida Gida sanyin guiwa ba, gwamnatin Kano ta tabbatar an gudanar da zaben cikin lumana.

Wannan na nuna irin ginshikin da jagoran kwankwasiyya, Inijini Rabi'u Musa Kwankwaso, ginshiki ne mai inganci wajen tafiyar da tsarin siyasa gamsasshiya ga al'umma.

Shugaban, ya nemi wadanda suka samu nasara a wannan zaben da su gina shugabancin su akan adalci, wadda manufar kwankwasiyya shi ne inganta rayuwar al'umma, ta fuskar ilimi, samar da ayyuka ga al'umma dan bunkasa tattalin arzikin kasa, tsaro da kiwon lafiya.

Hon. Awwal Goma, ya cigaba da cewar jagora yayi bayani a baya, cewar zaben 2027 mai zuwa, NNPP za ta kawar da jam'iyyar APC akan karagar mulkin kasar nan, abinda jagora ya fada bayan samun nasarar APC a 2023 sun bayyana, domin taron jama'a ne masu yunkurin sun kai ga madafun iko ba tare da wata manufa ba, yau kowani dan Nijeriya shaida ne in ban da kokuwar tara abin duniya ba abinda suka sanya a gaba.

Yau, a kasar nan ne mutum mai karamin karfi bai san hanyar da zai iya cin abinci sau uku ba, amma kullun gwamnatin na kara kakabo hanyoyin tsadar rayuwa ga talaka, in har katin kuri'ar talaka na da muhimmanci, kuma tabbas da gaske yake wannan halin da yake ciki a yau, ta ishe shi, al'ummar kasa ba su da kima a idon gwamnatin nan, yayan jam'iyyar ba su da kima a idon gwamnatin nan, to maganar jagora, Injiyini Rabi'u Musa Kwankwaso, raskwana uban lissafi zai tabbata.

Ba mu taba ganin tsarin siyasar da aka mayar da yan kasa bayi, da suka kasa tsayuwa da kafarsu wajen dogaro da kai ba,  tsare tsaren gwamnatin tamkar tsarin mulkin kama karya, shekara daya da wata shidan su akan karagar mulki tamkar shekaru uku ne da watanni shida da kowa ya kagara ayi zabe su tattara kayan su, gaskiya tun dawowar tsarin dimukuradiyya ba mu taba ganin mulki irin wannan ba, domin wannan tsarin tsari ne kamar wadda ba zaben ta aka yi da kuri'un talakawa ba, wannan salon mulkin APC da ta shinfidawa kasar nan ya sabawa hankali.

Jam'iyyar NNPP bisa tsarin Kwankwasiyya, za ta tabbatar a siyasa mai zuwa ta ajiye mutane masu amana, masu kishin kasa da cigaban kasa domin samun nasarar zabe daga sama har kasa.

A shirye muke duk wanda ya taka rawa, a Jam'iyyar NNPP a jihar nan, da mu hada karfi da karfe dan yin abinda ya kamata dan ganin mun kawo sauyi akan wannan tsarin siyasa na bautar da al'umma.
Saboda haka, muna kira da babban murya musamman ga wadanda suka shirya gwagwarmayar kwatan yanci da gaskiya da su tabbatar sun shigo wannan tsarin na kishin kasa ta jam'iyyar ANNPP kwankwasiyya, mun ga yadda ta kaya a jihar Kano, da yardar 2027 NNPP za ta mamaye kasar nan ta da samun gabala a zabuka masu zuwa.

No comments