Daga Awwal Umar Kontagora An yi kira ga talakawan arewa da su yi hakuri da nemarwa kan su hanyoyin walwale matsalolinsu, su daina baiwa shug...
Daga Awwal Umar Kontagora
An yi kira ga talakawan arewa da su yi hakuri da nemarwa kan su hanyoyin walwale matsalolinsu, su daina baiwa shugabannin su damar juya kwakwalen su domin shugabannin ba suna fada da gwamnati akan su ba ne. Wani dattijo mai fashin bakin harkokin yau da kullun kuma dan siyasa, Alhaji Hamza Yanga Buba ne ya bayyana hakan ga manema labarai a minna.
Yanga Buba, ya cigaba da cewar idan ka cire zamanin su Sir. Tafawa Balewa, da Sardaunan Sokoto, marigayi Ahmad Bello, ba wani shugaba a arewa da za ka iya nuna wani aikin cigaban kasa da ya kafa wanda talaka zai anfana. Kuma bisa kisasi kashi saba'in cikin dari na mulkin kasar nan duk yan arewa ne.
Tun yaushe arewa ke fama da matsalar Boko Haram, yau ga matsalar yan ta'addan daji masu farwa mutane suna garkuwa da su, babu wani shugaba daga kan gwamna har zuwa sarakunan gargajiya da suka fito suka nuna rashin amincewarsu sai siyasa idan tazo zasu fito kafafen yada labarai suna tada jijiyar wuya saboda manufar cin zabe.
Mun ji sun yi taro a Kaduna sun nuna damuwarsu akan matsalar wutan lantarki, amma ba su iya nuna damuwarsu kan daukar matakin gaggawa na kawo karshen rashin tsaro a arewa ba duk da irin din bin hasarar rayuka da dukiyoyin da talakawa ke yi a kullu yau min.
Lokaci yayi da talakan arewa zai bude idonsa ya fahimci cewar wadannan manyan ba suna tada jijiyar wuya akan shi ba ne, wata boyayyar manufarsu ce kawai na son cigaba da damawa a cikin harkokin gwamnati ya dame su.
Kashi saba'in da biyar cikin dari marasa ayyukan yi matasan arewa ne, kuma koda wata dama ta samu na samun alheri masu kiran kan su da sunan manya suna fafutukar yadda yayan su ne kawai zasu iya cin wannan garabasar, hakan ne yasa da gangan suka lalata tsarin makarantun boko na gwamnati dan ganin kamar yadda suka bautar da talaka a rashin aikin yi, yayan su sun cigaba da taka wannan rawar.
Yau, idan ka duba ko noma da talaka ke yi domin ya samu damar daukar dawainiyar kan sa da iyalansa na shirin gagararsa, saboda matsalolin tsaro da tsadar rayuwa.
Saboda haka, ina baiwa yan uwana talakan arewa shawara, da su guji duk wani tuggun da ake shiryawa dan yiwa gwamnati bore domin idan ya faru kasar ta lalace zasu iya kwashe iyalansu su bar kasar mu kuma talaka su bar mu cikin ja'iba, mun ga abinda ya faru nan baya kan zanga zangar lumana na cire tallafin man fetur, da yawan yayan talakawa musamman a jihar Kano, da wasu jahohin arewa na garkame a gidajen yari har yanzu.
Ba yadda arewa za ta cigaba muddin ba a samu shugabannin da zasu iya zama garkuwa ga talakawa ba, a tsarin ilimi an wuce mu, a kasuwanci ma an wuce mu, haka a shugabanci an bar mu a baya, yau idan aka samu dan majalisa daga matakin tarayya zuwa jiha da ya tashi tsaye akan manufar kare talakan arewa, shugabannin nan zasu kirkiro yarfe da zasu yi mai dan batanci gare, alhalin sun nade kafa a gidajen su suna ta rayuwa da kudaden rashawa da iyalan su.
Wajibin mu ne, talakawan arewa mu bude idanun mu, mu fito mu fadawa junan gaskiya, tare da nuna masu rashin amincewar mu da nagartarsu, ba ayyukan yi ga matasa, ba tsarin ilimi mai inganci, babu tsarin kiwon lafiya mai nagarta, sannan ga tsadar rayuwa da muke fama da shi a arewa.
No comments